An bayyana Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i a matsayin dakakken gwamna mai bin doka da oda wanda bai jin tsoron sabawa da kowa matukar ya sabawa doka. Sarkin Kagoma, Kpok Gwom Paul Zakka Wyom ne ya bayyana haka a fadarsa da ke Fadan Kagoma a karamar hukumar Jama’a da ke kudancin jihar Kaduna, yayin da yake karbar tawagar ’ya’yan jam’iyyar APC da su ka kai masa ziyara a fadar.
Kpok Gwom, ya ce Malam Nasir El-Rufa’i yana dora Jihar Kaduna ne a kan kyakkyawan turbar da jama’a za su dade suna amfana da ita inda ya ce ba lallai ne yanzu a gane haka ba saboda gaggawa da mutane su ke yi.
“Kwadayin abin duniya da jahilci da rashin sanin ya kamata su ne abubuwan da za su sa mutum ya kasa gane wanene El-Rufa’i. Irin matakan da ya dauka wajen samar mana da zaman lafiya da kuma yadda yake tafiyar da tattalin arzikin jihar Kaduna abin a yaba masa a kai ne,” in ji shi
Sannan sarkin ya nuna takaicinsa a kan wadanda su ma’auninsu na gane kyakkyawan shugabanci shi ne ga duk shugaban da zai rika raba musu kudi ko kuma wadanda su ke yin siyasa don a nada musu ‘ya’yansu a matsayin kwamishinoni ko sakatarrori ko wasu mukamai dabam.
A lokacin da ya ke gabatar da makasudin ziyarar tasu tunda farko, Shugaban Jam’iyyar ta APC na karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Ibrahim Aliyu (Koli), ya ce sun zo ne don tallata jam’iyyarsu da ’yan takararsu a zabubbukan kananan hukumomin jihar Kaduna da ke tafe don haka su ka zo neman albarkar sarakunan yankin karamar hukumar.
Daga cikin ’yan tawagar da su ka yi kewayen akwai shugaban masu ruwa da tsaki na APC reshen karamar hukumar Jama’a, Ambasada Joshua Ishaya da mai rufawa ’yar takarar shugabancin karamar hukumar Jama’a na APC, Kwamred Cecelia Musa, baya a matsayin mataimakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Abubakar Sadik Dahiru inda su ka bayyana manufarsu tare da neman albarka da addua’ar sarakunan.
Sun kai irin wannan ziyara fadar sarakunan Godogodo da Bade da Kagoma da Kaninkon da Fantsuam sannan su ka karkare a fadar mai martaba sarkin Jama’a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II.