Fadar Vatican ta sanar da Robert Prevost a matsayin sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis.
Sabon fafaroman wanda shi ne na farko daga ƙasar Amurka kuma wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya.
- Ficewar ’Yan Majalisa 3 a PDP: Raɗɗa ya halarci zauren Majalisar Wakilai
- An kama mutum 6 da ake zargi kan garkuwa da mutane
Robert Prevost zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin – wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV).
Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru.