✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Douye Diri na PDP ya sake lashe Zaɓen Bayelsa

Mista Diri ya samu wa’adi na biyu ne bayan ya lashe zaben da ƙuri’a 175,196.

Gwamnan Bayelsa kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP, Douye Diri, ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.

Mista Diri ya samu wa’adi na biyu ne bayan Baturen Zaɓe Farfesa Faruq Kuta ya bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri’a 175,196.

Ɗan takarar adawa na APC, Timipre Sylva, shi ne ya zo na biyu da ƙuri’a 110,108, sai kuma Udengs Eradiri na jam’iyyar LP a mataki na uku da ƙuri’u 905.

Sakamakon ƙaramar hukuma biyu na Kudancin Ijaw da Brass ne suka jawo ɗage tattara sakamakon har zuwa Litinin bayan an bayyana na ƙananan hukumomi shida cikin takwas a ranar Lahadi.

Turawan zaɓe na wasu ƙananan hukumomi sun bayar da rahoton soke zaɓe a rumfunan zaɓe da dama saboda hatsaniya, da garkuwa da mutane, da sace malaman zaɓe.

Kazalika, da yawa daga cikin wakilan jam’iyyun da ke cibiyar tattara sakamakon sun yi watsi da sakamakon da aka gabatar tun ranar Lahadi, amma babban baturen zaɓe na jihar ya nemi su kai ƙorafinsu ga INEC a hukumance.

Zaɓen na Bayelsa ya fuskanci hatsaniya tun kafin fara kaɗa ƙuri’a, inda aka yi garkuwa da wata jami’ar hukumar zaɓe ta INEC kafin daga baya a sako ta.

INEC ta sake fitar da sanarwar cewa an yi garkuwa da wasu jami’an nata a Karamar Hukumar Brass, waɗanda ba ta bayyana adadinsu ba.