✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Uwa ta kashe ’yarta mai watanni 11 a Binuwai

Ana zargin wata matashiya da kashe ’yarta mai watanni 11 ta hanyar ba ta guba a Karamar Hukumar Logo ta Jihar Binuwai.

Ana zargin wata matashiya da kashe ’yarta mai watanni 11 ta hanyar ba ta guba a Karamar Hukumar Logo ta Jihar Binuwai.

Matashiyar ta shiga hannu ne a ranar Asabar a yayin da take kokarin jefar da gawar yarinyar, inda matasa suka damke ta suka mika ta ga ’yan sanda a unguwar Abeda-Mbadyul.

Jami’in yada labaran karamar hukumar Logo, Paul Pevikyaa, ya yi zargin maganin kashe ciyawa matashiyar ta ba wa ’yar tata ta kashe ta.

“Ta ce ta saurayinta ne ya yi mata cikin shege ta haifi ’yar, amma sai ya yi watsi da su, ita ke shan wahalar kula da ’yar, shi ya sa ta ba ta guba ta mutu,” in ji Pevikyaa.

Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Binuwai, SP Catherine ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce rundunar na gudanar da bincike.

Wani mazaunin yankin ya yi kira da a hukunta matar, wadda wasu jami’an lafiya suka yi zargin na fama da tsananin damuwa.

Wani mai fada a ji a yankin ya ce a cikin daren Juma’a ne ’yar ta kamu da rashin lafiya, cikin kimanin awa biyu ta ce ga garinku nan.

“Babu wanda ta sanar a cikin makwabta ba, kuma sanin kowane cewa idan abun da ya fi karfin mutum ya same shi a cikin dare, yana neman makwabta su kawo masa dauki, ita kuma ba ta yi hakan ba.

“Da gari ya waye kuma sai ta yi kokarin ta je binne ’yar; don haka dole a sanya mata alamar tamba, in ba haka ba, me take kokarin boyewa?” in ji shi.