Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe ya yaba bisa ga yadda jama’a suka fito don kada kuri’un su a kan lokaci ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Buni ya bayyana hakan ne jim kadan ya kada kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba ta 004 da ke mazabar Bulturam /Yarimari ta garin Buni Gari a Karamar Hukumar Gujba.
- Wasu mata sun sha da kyar a wajen zabe a Kano
- INEC da ’yan sanda sun shirya magudi a zaben Kano —Kawu Sumaila
A cewar Gwamna Buni, bisa ga yadda ya ga mutane sun fito don kada kuri’unsu a farar safiya fiye da yadda suka yi zaben Shugaban Kasa da ya gabata abin a yaba ne matuka.
Ya kuma yaba wa Hukumar Zabe ta Kasa INEC bisa ga yadda ta yi cikakken shiri wajen gudanar da wannan zabe musamman yadda na’urar tantance masu zabe ta BVAS ta yi aikin ta ba tare da samun wata tangarda ba.
Gwamna Buni ya yi fatan samun zabe mai inganci yadda al’umma za su aminta da shi.