✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Yobe za ta yi wa ma’aikata da ’yan fansho ƙarin kuɗi

An bukaci ma'aikatan da su jajirce wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ake bukata.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya sake amincewa da ƙara biyan Naira 10,000 ga ma’aikatan gwamnati da kuma Naira 5000 ga ’yan fansho a jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da babban jami’in yada labarai a Ofishin Shugaban Ma’aikatan jihar, Alhassan Sule Mamudo ya fitar.

Takardar mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban ma’aikatan jihar, Hamidu M. Alhaji, ta ce amincewar ya biyo bayan karin albashin ma’aikata da aka yarda da shi a baya na tsawon watanni shida wanda ya fara a watan Fabarairu.

Ya kara da cewa, “jimillar kudaden da aka amince da su domin biya sun kai Naira miliyan dari shida da casa’in da biyar da Naira dubu dari tara (N695, 900, 000.00) wanda a ciki an ware Naira miliyan dari uku da ashirin (N320, 000, 000.00) ga ma’aikatan jiha da ‘yan fansho.

“Sai Naira miliyan dari uku da saba’in da biyar da Naira dubu dari tara (N375,900, 000.00) ga ma’aikatan kananan hukumomi da ’yan fansho su ma na kananan hukumomi.

“Wannan matakin an yi shi ne don rage tasirin wahalhalun da ake fama da su a yanzu da kuma bayar da agaji a ma’aikatan da ’yan fansho a yayin bikin karamar sallah mai zuwa.

“Sai dai kuma a cewarsa ba za a aiwatar da biyan albashin watan Maris na 2024 tare da wadannan kare-kare guda biyu ba, duk da haka, za a biya karin Naira dubu goman watan Maris na 2024 da kuma karin kyautar dubu goman ne a tare ko kafin makon farko na watan Afrilu 2024.

“Ana sa ran ma’aikatan za su mayar da wannan karamcin na Gwamna ta hanyar jajircewa wajen ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ake bukata kamar yadda Hausawa ke cewa yaba kyauta tukwici.”