A makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya mika mabudin sabuwar mota kirar Toyota Corolla, don cika alkawarin da ya dauka na bai wa wata miskiniya mai suna Fatima Musa kyautar mota a fadar gwamnatinsa da ke Lafiya.
Gwamnan ya ga matar ce ’yar shekaru 25 ’yar asalin Jihar Bauchi a garin Lafiya, yayin da wani ke dauke da ita a baro, inda a nan take ya ba da umarnin tsaida tawagar tasa, sannan ya ce a kawo ta kusa da shi don su yi magana.
Bayan an kawo ta ya fahimci tana da nakasar hannuwa da kafafu duka baki daya, ba ta iya tafiya sai tare da taimakon ’yan uwanta, sannan uwa ce ga yara biyu. Sai gwamnan ya yi mata kyautar kudi sannan kuma ya tambaye ta ko akwai wani taimako da take so daga gare shi, inda ita kuma ta sanar da shi burin da ke gare ta na son mallakar motar da za a rika zagayawa da ita a maimakon baro.
Cike da murmushi a fuskarsa ya ce da ita: “Burinki ya cika na mallakar mota, don haka a kawo ki gidan gwamnati gobe zan ba ki motar. Dukkanmu daya ne, sannan dole ne mu taimaki gajiyayyun cikinmu kamar yadda Allah Ya yi umarni.”
Fatima ta fashe da kuka a yayin da take karbar mabudin sabuwar mota gami da kudin mai Naira dubu 200 da kuma na biyan direban da zai dauke ta har zuwa mahaifarta ta Bauchi cikin ’yan’uwanta, sannan daga bisani ta yi wa gwamnatin addu’ar fatan alheri a duniya da lahira.
A wani abu makamancin haka kuma, wata yarinya ’yar makarantar sakandare mai suna Mama Likita mai kimanin shekara 20 da ke kauyen Gurmin Tagwaye da ke yankin karamar Hukumar Akwanga a jihar ta Nasarawa, ita ma Allah Ya yi mata gyadar dogo a ranar Asabar din da ta gabata, inda gwamnan ya hango ta a daidai lokacin da yake dawowa daga garin Wamba, tana ketare hanya a cikin keken guragu, inda ya umurci direbansa ya tsaya.
Nan take ya same ta da kansa, inda bayan hira da gwamnan ya yi da ita na wasu mintuna, ya tambaye ta abin da take so ya yi mata. Ta amsa masa cewa tana so ta zama Unguwar Zoma a rayuwarta. Gwamnan ya tuntubi mahukuntan wani karamin asibiti da ke kauyen na Gurmin Tagwaye cewa su dauke ta aiki cikin gaugawa.
Daga bisani kafin ya wuce, ya kuma ba ta kyautar wasu kudi da ba a bayyana adadinsu ba. Ita ma nan take ta fashe da kuka, tana murna dangane da karamci da ba ta yi tsammaninsa ba da gwaman ya yi.
Gurguwar ta yi godiya dangane da kyawawan ayyukan da a cewarta gwamnan yake yi wa nakasassu a jihar. Ta kuma yi addu’ar Allah Ya saka masa da alheri.