✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Almakura ya bai wa nakasasshiya kyautar mota

A yau ne Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya mika mabudin sabuwar mota kirar Toyota Corolla, don cika alkawarin da ya dauka na bai…

A yau ne Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Almakura ya mika mabudin sabuwar mota kirar Toyota Corolla, don cika alkawarin da ya dauka na bai wa wata miskiniya mai suna Fatima Musa kyautar mota a fadar gwamnatinsa da ke Lafia.

Gwamnan ya ga matar ce yar shekaru 25 ‘yar asalin Jihar Bauchi a City Centre da ke Lafia, yayin da wani ke dauke da ita a baro (wheelbarrow), inda a nan take ya bada umarnin tsaida tawagar tasa, sannan ya ce a kawo ta kusa da shi don su yi ma

Bayan an kawo ta ya fahimci ta na da nakasar hannuwa da kafafu duka baki daya, ba ta iya tafiya sai tare da taimakon ‘yan uwanta, sannan uwa ce ga yara biyu. Sai gwamnan ya yi ma ta kyautar kudi sannan kuma ya tambayeta ko akwai wani taimako da take so daga gare shi, inda ita kuma ta sanar da shi burinta shi ne ta mallaka motar da za a rika zagayawa da ita a maimakon baro.

Cike da murmushi a fuskarsa ya ce da ita, “Burinki ya cika na mallakar mota, don haka a kawo ki gidan gwamnati gobe zan baki motar. Dukkanmu daya ne, sannan dole ne mu taimaki gajiyayyun cikinmu kamar yadda Allah Ya yi umarni” in ji Gwamna Alamakura.

Fatima ta fashe da kuka a yayin da take karbar mabudan sabuwar motar gami da kudin mai da kuma na biyan direban da zai dauke ta har zuwa mahaifarta ta Bauchi cikin ‘yan’uwanta, sannan daga bisani ta yi wa gwamnatin addu’ar fatan alheri a duniya da lahira.