Maganin riga-kafin COVID-19 da Cibiyar Kimiyyar Tsirrai ta Kwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya a Kasar China ta samar ya shiga matakin gwaji na biyu a kasar.
Kafar yada labarai ta kimiyya da fasaha ta (Science and Technology Daily Report) ta sanar da haka a ranar Asabar 20, ga watan Yuni.
Gwajin da aka yi a matakin na biyu a yankin Kudu maso Yammacin Yunnan, ya gano tasirin maganin riga-kafin wajen bunkasa garkuwar jiki tare da rashin illarsa a cikin dan Adam.
Zuwa yanzu dai maganin riga-kafin COVID-19 biyar ne aka amince a yi gwajinsu a kasar China wato kaso 40 bisa 100 na maganin riga-kafin cutar a fadin duniya, a cewar ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar.