✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwajin kanjamau dole ga masu shirin aure

kokarin da ake yin a shawo kan sababbin cututtuka da hana yaduwarsu, Gwamnatin Tarayya ta fito da sabon tsarin yaki da cutar kanjamau da mai…

kokarin da ake yin a shawo kan sababbin cututtuka da hana yaduwarsu, Gwamnatin Tarayya ta fito da sabon tsarin yaki da cutar kanjamau da mai karya garkuwar jiki (HIb/AIDS). Tsarin ya fito da shirin tilasta masu shirin yin aure, ga Musulmi da Kirista su yi gwaji a daukacin fadin kasar nan. Daraktar Hukumar Yaki da Cutar kanjamau da Mai Karya garkuwar jiki (HIb/AIDS) da tarin fuka (TB) da kuturta da zazzabin cizon sauro ta Jihar Bauchi, Dokta Yakubu Abubakar, wand aya bayyana sabon shirin yaki da cutar na kasa, a wani taro da aka gudanar a Abuja, ya bijiro da yadda cutar ke yaduwa a tsakanin jiha zuwa jiha, da kuma matakin kawar da kanjamau (HIb). Sai dai Abubakar bai bayar da cikakken bayani kan yadda za a aiwatar da tsarin.
Baban Jami’in Kula da Shawo kan cutar da Kyautata Zamantakewa da sabon tsarin sadarwar sauyin dabi’a, Misis Uduak Daniel, ta ce bambancin tsoho da sabon tsarin, shi ne a sabon tsarin al’ummomin karkara za su shigo a dama da su.
Abin damuwa a nan, shi ne, matsayin tursasawa a dokar likitanci da halin zamantakewar al’umma, har ma a tsarin agajin gaggawar kula da lafiya na duniya, game da cutar kanjamau da mai karya garkuwar jiki. daukar matakan kula da lafiyar al’umma na da muhimmanci, amma yin dokar gwajin kanjamau a matsayin sharadin daura aure, a tsakanin baligai biyu da suka amince wa juna, wannan na nufin hukuma ta shiga rayuwarsu, tun da al’amari ne da ya shafi kebantacciyar harkar rayuwa. Wasu na takaddama kan cewa tilasta yin gwajin keta haddin ‘’yan kasa ne, da ke da ’yancin hana shiga cikin rayuwarsu. Wasu kuwa na da ra’ayin cewa irin wannan shirin a kan kowa da kowa zai yi rugurugu da kokarin shawo kan cutar anjamau, saboda za cusa wa al’umma tsoron nuna musu kyara.
Wannan shiri ana iya cewa yana da kyau wajen magance yaduwar wannan cuta mai kisa fat daya. Sai dai akwai bukatar a yi dokar da za ta tabbatar da nasarar aiwatar da shirin. A kuma yi takatsantsan wajen samar da irin wannan dokar, bisa la’akari da bambance-bambancen addinai da al’adu a cikin al’umma Najeriya. A fito da tsarin fadakarwa ga al’umma, don wayar da kan wadanda ke tattare da hadarin kamuwa da cutar, inda za a nuna musu alfanun manufofin da ke tattare da yin gwajin kafin aure. Tsare-tsare irin wadannan suna yin tasiri ne iodan aka aiwatar da su ta hanayar lalamar jan ra’ayi.
Baya ga gwajin cutar kanjamau, ya kamata gwamnati ta yi fadakarwa ga al’umma, tare da bai wa masu shirin aure kwarin gwiwar yin gwaje-gwajen kula da lafiya da suka hada da binciken ciwon suga da asarar zubar jini da makamantansu.
A shekarar 2013, Najeriya ta dauki nauyin babban taron Tarayyar Afirka kan Cutar kanjamau da mai karya garkuwar jiki da taron fuka da zazzabin cizon sauro. Al’amuran da aka tattauna, kuma shugabannin kasashe suka rattaba hannu a kansu, sun bijiro da dimbin kalubalen da ke tattare da kawar da wadannan cututtuka. Bayanan sun nuna damuwa kan karancin kudin da za a yi amfani da su wajen inganta harkokin kula da lafiya, ta yadda za a shawo kan yaduwar cututtukan a tsakanin kasashen da ke cikin tarayyar. Talauci da rikice-rikice a wadannan kasashen tarayyar da suka hada da Najeriya, su ke haifar da cikas wajen aiwatar da shirin shawo kan cututtukan, su kumas nakasa harkokin kula da lafiya.
Wannan sabon tsari na gwamnati ya kamata ya kauce wa duk wani tasgaro, a fito da ingantaccen tsarin tilasta yin gwaji, inda gwamnati za ta dauki nauyin, musamman a daidai wannan lokacin da ya akmata a karfafa gwiwar mutane da yawa su rika zuwa wurin gwajin.
Kauce wa yin lalata ga wadanda ba su yi aure ba, shi ne abin da za a bijiro da shi gaba-gaba a wajen wayar da kan al’umma. Don a cimma manufar Tarayyar Afirka (AU) wajen shawo kan yaduwar cutar kanjamau da sababbin cututtuka na da shekara ta 2030, ya kamata gwamnati ta gaggauta fara amfani da ingantaccen tsari kawar da cutar, musamman a tsakanin matasa da rukunin al’umma, wadanda ke tattare da hadarin kamuwa da cutar. Kamar yadda Abuja na 2013 ya alkawarta, Najeriya tamkar sauran kasashen kungiyar, akwai bukatar ta kara kaimi wajen samar da maganin karya lagon cutar kanjamau (anti-retrobiral). Ita kuwa munfar da za a cimmawa a dogon zango, za ta mayar da fifiko ne wajen gudanar da bincike don samar da rigakafin cutar.