Assalamu Alaikum. A wannan makon za mu gabatar da bayani kan tanade-tanade da shirye-shiryen da ya kamata ma’aurata su yi don tarbar watan Ramadan. Da fatan Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Guziri Na 1: Inganta Niyya Da kudurta Alheri: Abu na farko, kuma mafi alfanu shi ne, ma’aurata su daura kyakkyawar niyyar cin ribar wannan muhimmin lokaci don dacewa da alheran da ke cikinsa. Za su yi haka ne ta hanyar kudurta dagewa wajen yin ayyukan ibada da na kyautatawa don su samu dacewa da rahma da gafarar da Allah Ya yi tanadi ga bayinSa da suka aikata kyawawan ayyuka a cikin Ramadan.
Haka kuma idan ma’aurata suka kudurta yin ayyukan alheri a Ramadan, wannan zai kara musu taushin zuciya, ya kuma bude masu hanyar karuwar imani. Kamar yadda Annabi SAW Ya ce, wato dukkan ayyuka ba su tabbata sai da niyya, don haka duk wani aikin da ma’aurata ke son aiwatarwa a Ramadan, to sai su fara da kulla masa kyakkyawar niyya, su tabbatar niyyar na cikin zuciyarsu, sannan kullum su rika jaddada wannan niyyar, ko da ta hanyar rubatawa a takarda don karantawa kullum, har sai wannan niyya ta zama babba, kuma sanannen kudiri cikin zuciyarsu, wannan zai zama garanti gare su na cewa lallai in Ramadan ya tsaya, to za su samu nasarar aiwatar da dukkan ayyukan alherin da suka yi niyya.
Haka kuma ma’aurata suna iya rubuta kudirorin da suke son aiwatar da su cikin Ramadan a takarda a tare ko daban-daban, sai su rika yawan karanta su don jaddada su cikin ma’aikatar hankalinsu. Ga misalan wasu kudirori masu kyawu da ya kamata ma’aurata su yi kokarin jaddada su da aiwatar da su cikin Ramadan:
• Yin amfani da watan Ramadan don neman kara kusanci ga Allah SWT da kuma kara kusantar juna.
• Yin hakuri da kawar da kai ga kura-kuran juna.
• Gyara tare da kara kyautata dangantakar auratayyarsu.
• Hada kai da taimakon juna wajen yin bautar Allah.
• kara wa juna karfin gwiwa wajen dagewa ga yin ayyukan bautar Allah.
• Taimakon juna wajen kula da gida, musamman ta fannin hada kayan buda baki da sahur da kuma kula da tarbiyyar yara.
• Yin kokarin kawar da wata dabi’a marar kyawu. Daina sabon Allah ko wani laifi da ake yawan aikatawa a cikin gidan, ko daya daga cikin ma’aurata.
• Yanke kallon fina-finai ko wasannin banza a talabijin a cikin wannan wata gaba daya.
• Daina almubazzaranci, watau wulakanta abubuwan rahmar da Allah Ya ni’imta bayinSa da su: kamar abinci da kayan sawa da ruwa da kayan amfanin gida da kuma lokaci.
Da sauran kudirori masu kyau da suka dace da ma’aurata da yanayin rayuwarsu.
Guziri Na 2: Gyara Zuciya: Duk daya daga cikin ma’aurata da ya ji yamutsi ya yi yawa cikin zuciyarsa, to kada ya yarda Ramadan ya riske shi a haka, ya yi kokarin sama wa zuciyarsa natsuwa da aminci ta wadannan hanyoyin:
• Yawan karanta kur’ani safe da maraice, ka’in da na’in. Tabbas duk mai yin haka, cikin dan kankanen lokaci, zai nemi wannan yamutsi ya rasa, zai ji hankalinsa ya kwanta, kuma tunaninsa ya daidaita. Kamar yadda Allah SWT Ya sanar mana cikin Littafinsa mai Girma, Suratul Ra’ad, Aya ta 28:
“Wadanda suka yi imani, zukatansu sukan natsu da ambaton Allah, to da ambaton Allah ne zukata suke natsuwa-”
Wannan ke tabbatar mana da cewa karatun kur’ani yana sa zuciya natsuwa da farin cikin da ba su misaltuwa, kuma yana tsabtace hankali da tunani da kuma shau’ukan cikinta.
• Kyakkyawar tuba: Wannan na samuwa ne lokacin da mutum ya yi tsananin nadamar laifukan da ya sabi Allah da su, ya ji haushin kansa, kuma ya ji nauyi da daudar zunubinsa, sannan ya koma ga Allah ya nemi gafara cikin nadama da kankan da kai ga Allah, sannan da yawan yin istighfari safe, rana da daddare, ka’in da na’in, ko shakka babu tuba irin wannan tana wanke zuciya daga daudarta, kuma tana saukar mata natsuwa da aminci.
• Sadaka/Kyauta: Yawan kyauta da yin sadaka ga mabukata yana saukar da farin ciki cikin zuciya, wannan wani sirri ne da masana kimiyya ma sun tabbatar da shi, don haka duk mai fama da yamutsin zuciya, sai ya yawaita yin kyauta kafin da kuma cikin watan Ramadan.
• Haka kuma ana gyara zuciya ta hanyar kawata ta da ayyuka masu kyau, raya ta da yawan tunanin Allah da kyautata zato gare Shi da kuma guje wa aikata ayyukan sabon Allah da munana zato ga Allah SWT da kuma guje wa mummunan tunani da munanan shau’uka.
Guziri Na 3: Gyara Da Shirya Muhalli: Babban bako, mai matukar muhimmanci zai bakunci gidan ma’aurata; don haka yana da matukar muhimmanci su yi dukkan shiri da ya kamata don yi masa tarba mai kyawu da ba shi mafi kyawun masauki a cikin gidansu. Don tabbatar da haka, sai su yi amfani da wadannan hanyoyi:
• Kwana biyu ko uku kafin Ramadan, sai a share gida gaba dayansa, a cire yana, a kwashe kwata; a rage tarkace, mai sauran amfani a kyautar ga masu bukata, marasa amfani a zubar a bola; sannan a rage like-like da kayan kawa, musamman hotuna da like-liken kwalliya masu daukar hankali lokacin ibada; sannan a gyara wuraren da siminti ya farfashe, musamman in ruwa na yawan taruwa a wurin; in kuma fentin gidan ya tsufa, kuma inda halin yin sabo, to sai a yi ga duka ko wani bangare mafi muhimmanci na gidan.
• A tanadi hanyar samun ruwan amfanin yau da kullum; in wani fanfo na bukatar gyara, ko rijiya na bukatar yasa, duk sai a yi kafin Ramadan.
• A tanadi hanyoyin samun haske da daddare, a canza kwan lantarkin da ya mutu, a tanadi fitila mai amfani da batiri, masu halin janareta su tabbatar da lafiyarsa, kuma su yi masa duk tanadin da ya kamata kafin Ramadan.
• A tabbatar cewa murhun da ake amfani da shi, na itace, risho ko na gas, ba shi da wata matsala, idan kuma yana da matsala a yi kokarin gyarawa kafin Ramadan, sannan a tanadi makamashin konawa, watau itace, kalanzir ko gas daidai gwargwadon hali.
• A tanadi dukkan kayan abinci daidai gwargwadon hali, sannan masu bukatar gyara sai a gyara su yadda da an zo amfani da su cikin Ramadan, kawai sai dai a sarrafa ba sai an tsaya gyarawa ba.
• A yi dukkan saye-sayen kayan Sallah da dinkunan Sallah tun kafin Ramadan, ta yadda in watan ya tsaya sai dai a mayar da hankali wajen ibada da bautar Allah kadai.
• A kaurace wa kallon talabijin ko sauraren kide-kide, sai na shirye-shiryen addini kadai; in kuma har ya kasance garin kallonsu za a kunno wasu tashoshin wasannin banza, to sai a dauke talabijin din gaba daya daga wajen kallon, har sai bayan Ramadan.
Guziri Na 4: Jadawalin Ramadan: Lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar bil Adama, rashin sarrafa shi yadda ya kamata na jawo wa dan Adam asara mai yawa da kuma ci baya a rayuwarsa. Don haka duk mai son ya ribaci dukkan alheran da ke cikin watan ramadan, dole sai ya tsara, ya kuma shirya lokacinsa ta hanyar yin abubuwan da suka dace a lokacin da suka dace. Abin da zai taimaka wa mutum cimma wannan shi ne, ta hanyar yin jadawalin lokacinsa. Yin jadawali da amfani da shi abu ne mai matukar muhimmanci, kuma mai tabbatar da cin nasara cikin rayuwa. Mu duba makarantu da manyan kamfanoni, amfani da jadawali shi ke dawwamar da kasancewarsu, idan ba su aiki da jadawali, cikin karamin lokaci za su samu matsala.
Yadda za a tsara Jadawalin Ramadan: Don samun sauki wajen tsarawa, sai ma’aurata su tsara ayyukan da suke son aiwatarwa a rana, a cikin sa’o’in da ke tsakanin lokacin sallolin farilla biyar; misali, sai a fara da ayyukan da ake son aiwatarwa a lokacin sahur. Misali, me za a yi bayan Sallar Asuba kafin Sallar Azahar; bayan Azahar kafin la’asar; bayan la’asar kafin magriba; bayan magriba kafin isha’i; bayan isha’i da tarawiy kafin lokacin sahur; sai a bi a cike wadannan lokuta da ayyukan da suka dace, kuma ana so a fara sa aikin da ya fi muhimmanci, ko wanda ya zama dole, sannan mai bi masa a muhimmanci, sannan mai bi masa har a hada duka.
Tun da ba komai ne ma’aurata ke yi tare ba, kuma ba ko da yaushe suke tare ba, ya kamata kowanne daga cikin ma’aurata ya kasance na da jadawalinsa, sannan kuma su yi wani na gida guda daya, wanda zai kunshi kowa da kowa har da yara duka. Don ganin alfanun da ke cikin yin jadawalin lokaci, DOLE sai ma’aurata sun ladabtar da kansu ga yin amfani da shi yadda yake, ba tare da tsallake wani aiki ba ko daukar aikin wani lokaci a kai shi wani lokaci, kuma dole su ladabtar da dukkan wadanda ke karkashinsu wajen yin aiki da jadawalin nan sau da kafa.
Guziri Na 5 Gyara Dangantaka: Yana da kyawu ma’aurata su yi kokarin gyara da inganta dangantakarsu kafin isowar Ramadan, da haka ne za su dace da cin ribar dukkan alheran da ke cikinsa. Su yi kokarin kara kusanci da shakuwa da juna da kuma kara karfafa zumuncin auren da ke tsakaninsu.
karin kyautata wa juna da yin hakuri da juna da sauran kyawawan abubuwa na dadada wa juna. Su zauna, su tattauna game da dangantakarsu, su yi afuwa ga juna, su toshe duk wata baraka da ke tsakaninsu don ya kasance in Ramadan ya zo, ba abin da ke gabansu sai more rahmar da ke cikinsa da yin ibada.
Guzirin Ma’aurata Don Ramadan
Assalamu Alaikum. A wannan makon za mu gabatar da bayani kan tanade-tanade da shirye-shiryen da ya kamata ma’aurata su yi don tarbar watan Ramadan. Da…