✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gurbataccen hayaki: Za a fara kwace motoci da injina

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara daure mutanen da motocinsu ko janaretocinsu ke fitar da gurbataccen hayaki. Darakta Janar na Hukumar Kula da Muhalli…

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara daure mutanen da motocinsu ko janaretocinsu ke fitar da gurbataccen hayaki.

Darakta Janar na Hukumar Kula da Muhalli (NASREA) Farfesa Aliyu Jauro ya ce duk wanda aka kama motarsa ko janaretonsa na fitar da gurbataccen hayaki to za ta hana shi amfani da ita, sannan a ci shi tara ko a hada da daure shi, gwargwadon girman laifinsu.

Da yake bude taron sanin makaman aiki ga sabbin kwararrun masana ingancin muhalli, Farfesa Jauro ya ce hukumar za ta rika lura da ababen hawa da janaretoci domin tabbatar da suna kiyaye dokokin kare muhalli.

Ya ce nan gaba za a kaddamar da shirin takaita fitar da hayakin ababen hawa da janaretoci domin takaita gurbacewar muhalli.

A cewarsa NASREA ba za ta yi wata-wata ba wajen kwace lasisin duk jami’in kula da muhalli da ta samu yana wasa da aikinsa a fadin Najeriya.