Kafin na shiga gundarin rubutun bari in dan yi waiwaye zuwa lokutan baya. A lokutan da suka shude a kasar Hausa ba a sanya tufafin da suke bayyana tsiraici ba, a lokacin za a ga ‘yan mata cikin shiga ta mutunci da kamala; a lokacin ba za a dinga ganin ‘yan mata cikin maza barkatai kamar yadda yake faruwa a yau ba, ko da ta kama za a yi cudanya tsakanin maza da mata a makarantu to za ka ga rayuwar Bahaushiya daban a cikinsu. Kuma za a ga duk inda mace Bahaushiya ta hada hanya da wani walau mutumin kirki ko na banza sai ya ba ta hanya gami da girmamata, sakamakon kamun kai da shiga ta kamala da take da ita.
A yau zamanin da mu ke ciki rayuwar ‘yan mata tana cikin wani mummunan hali, saboda idan muka yi duba zuwa zubi da tsarin rayuwar ‘yan mata a yau za sai mun zubar da hawaye, gaba daya sun canja dabi’unsu na asali zuwa kwaikwaiyon wasu kabilu da ba su fi su komai ba, Hausawa na cewa “kayan aro abin banza ne”. Sun buge da shafe-shafe da maimakon kwalliya ta biya kudin sabulu sai kilu ta ja bau. Wannan batu na malam Bahaushe haka yake, to sai in ce kalubalen ’yan mata, ya kamata su daina kwaikwayon wasu kabilu suna watsar da al’adunsu don babu wani abin burgewa ciki, kuma matan Hausawa ba za su taba burge wadanda ba Hausawa ba, don babu wani abu da zai burge su a tare da matan Hausawa, saboda ba su rike kwalliyarsu da al’adarsu ba, sun tsaya suna ta koyi da wadansu, sun kassara kayansu da kansu.
To idan matan Hausawa ba su sani ba, to su sani, sanin asali shi ya sa kare yake cin alli. Yau duniya ta canja sai ka girmama al’adarka ake yi da kai. Abin takaici ga doki har doki amma sai ka gan shi da kofaton sakaina, ma’ana za ka ga budurwa Bahaushiya ‘yar Bahaushiya amma sai ka ji yaren Hausar ma yana neman yi mata karanci wurin magana, ballantana kuma uwa-uba a zo ga maganar mene ne al’adarta, me ta sani game da kwalliyar Bahaushiya. Wani abin haushin sai ka sanya mace ta yi maka girki a nan za ka ga yadda ake girki hatta indomie da yawan mata ba su iya girkawa ba.
Idan ka ce mace ta yi maka tuwo dan Hausa kuwa a nan za ka ga kwaba, domin ba za ta iya ba, ta gama kokari ta yi maka dan malale (ruwa-ruwan talge), wannan shi ne a madadin tuwon, idan kuwa aka zo batun wasu kayan abincin sam ba ta san su ba don ba ta ga ana yi a gidansu ba.
Wani abin takaici kuma shi ne, yadda wasu daga cikin ’yan matan yanzu suka mayar da kansu ballagazaye ta hanyar siyan man shafawa mai canja launin fata, abin da ake kira da Turanci bilicin (bleaching).
To, a gaskiya wadannan abubuwan da ’yan mata suka azawa kansu sam ba zai haifar musu da da mai ido ba. Don haka shawara a nan ita ce su koma su binciki yadda al’adarsu take.
Illolin shafe-shafe
Shafe-shafe yana da illoli masu tarin yawa musamman ga ’ya mace. Na farko yakan canja wa mace launin fatarta. Wanda asalin fatar ita ke ba da kariya daga cututtuka da suke barazana ga kwayoyin halittar fata.
Za mu ci gaba.