✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gurbacewar Adabin Hausawa (2)

Fina-finai A game da fina-finai da yawaitarsu an yi rubuce-rubuce da ka-ce-na-ce game da su. Ga abin da Isa Sanusi yake cewa a makalarsa mai…

Fina-finai

A game da fina-finai da yawaitarsu an yi rubuce-rubuce da ka-ce-na-ce game da su. Ga abin da Isa Sanusi yake cewa a makalarsa mai taken: Fina-finan Hausa Ina aka dosa? Wannan a cikin mujallar Rana, fitowa ta 77:

“Ba sai an nanata ba, fina-finan Hausa suna tashe sosai a kasar Hausa da ma sauran sassan kasar nan inda Hausawa ke zaune. Ko’ina ka duba za ka ga shagunan saidawa ko kuma ba da hayar kaset-kaset na fina-finan Hausa. Ga shi kuma yara da manya duk na matukar sha’awar abin. In ka shiga tasha ko kasuwa sai ka ji wakokin fina-finan Hausa suna tashi ta ko’ina. Ga kuma fastocin fina-finan a kan tituna. Abin ba wai a birane ba ne har ma da karkara. Kafin bullowar fina-finan Hausa mun dogara ne ga kallon fina-finan kasashen waje, kamar na Amurka da China da Indiya da Japan da sauransu.”

Har wa yau, game da yawaitar fina-finai ga abin da wani marbuci ke cewa, wato Mauhammad Mujtaba Abubakar a cikin littafinsa da ya gabata:

“Hakika miyagun rubutattun tatsuniyoyi su ne suka haifi munanan fina-finai a wannan fage na majigi, fina-finan Indiya sun fi shahara da jigon soyayya. Akasarin fina-finan Amurka da sauran kasashen Yammacin Turai su suna kasancewa a kan jigon jarunta da na ta’addanci kamar sata da fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi da fyade da zinace-zinace da kuma luwadi da madigo.”

Haka kuma wani marubuci mai suna Farfesa Abdalla Uba Adamu ya yi bayani game da yawaitar fina-finai da yadda ake ganinsu a idanun jama’a. Ga yadda ya ce a cikin wata makala da ya rubuta a cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo 18/2/2002:

“Babu inda wannan zargi ya fi karfi illa harkar cinikayyar shakatawa, tun ma ba ta hanyar samar da fina-finai ba. Babbar illa a zamantakewar dan Adam ita ce, nuna yamutsuwar jinsin maza da mata, kamar ta hanyar jima’i. Sa’annan sai taratsi ta hanyar kashe-kashe da kuma sace-sace da shan kwayoyi iri-iri. Wadannan duk ana ganin cewa abubuwan yau da kullum ne a rayuwar Amurkawa, saboda haka babu mamaki idan suka rika fitar da su a fina-finansu. A dalilin haka ne wannan tunani ya ci gaba da nuna babu dokar Allah da ta dattaku a kasar Amurka, kowa yadda ya ga dama yake yi.”

Baya ga wadanan abubuwa da suka gabata da ake ganin su ne suka sa ka-ce-na-ce ta yawaita a kan fina-finan Hausa, akwai wadansu da masana Adabin Hausa da ke korafi a kansu domin kasancewarsu sun saba wa al’adun Hausawa. A cikin  makalarsa a mujallar Rana fitowa ta 79 mai taken “Waka A Fina-Finan Hausa Kayan Aro” Isa Sanusi cewa ya yi:

“Amma lokacin da fina-finan Hausa suka fito da salon surka wakoki a fina-finansu sai aka yi ta ka-ce-na-ce. Wadansu ma har suka ce yin hakan shiririta ce, dalilinsu kuwa shi ne abin bai dace da dabi’u da al’adun Hausawa ba. Wannan haka yake domin duk wanda ya kalli irin wadannan wakoki a fina-finan Hausa zai ga abin sam ba tsari, ya yi bambarakwai, kai ka ce an yi haka ne. domin basira ta toshe.…” A lokacin da aka fara wannan salo abin ban haushi, abin dariya. Domin za ka ga kato da budurwa suna zagawa da fulawa suna cirar fure, suna rausayawa da kuma rangwada. Abin har yakan fita daga kan jama’a….”

Wannan marubuci har wayau, ya fadi korafe-korafen jinsunan jama’a  game da fina-finan. Wannan a cikin makalarsa da ke cikin mujallar Rana fitowa ta 77, mai taken: FINA-FINAN HAUSA INA AKA DOSA? Wannan kamar yadda iyaye ke ganin ana son a lalata musu tarbiyyar ’ya’ya ne da wadannan fina-finai. Haka kuma akwai korafi na malaman addini da ke ganin akwai lokuta da sau da yawa akan siffanta malamai da bokaye da tsibbace-tsibbace. Haka akwai masu yawaita kawo ayoyin Alkur’ani a gurbace.

Haka har wa yau wani marubucin ya nananta abin da mutane ke korafi a kansa game da fina-finan. Wannan marubucin kuwa shi ne Abubakar Sadik Yusuf Kano, a cikin makalarsa da ke cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta ranar 6/9/2001. Ga abin da yake fada:

“Duk wanda ke biye da shirye-shiryen fina-finan Hausa, ba zai yiwu ya rasa ganin wani abu da ya mamaye fina-fanan ba, wanda za a iya cewa ya shafi ainihin jigogi ko kuma sakonnin da ke cikin fina-finan. Wannan abu bai wuce yadda samari da ’yan mata ke wage bakuna suna wake-wake da raye-raye kamar Indiyawa ba. Ba wani fim a halin yanzu da za ka ga an shigar da shi kasuwa, ba tare da wasu wakoki ba, ko dai a tsakanin budurwa da  saurayi, ko tsakanin miji da mata, ko makamatan haka. Masu shirya wadannan fina-finai, suna masu ra’ayin yin haka saboda dalilai da suka hada da:

Abin da yawancin masu kallo ke bukata ke nan.

Yana taimakawa wajen cika fim da sauri.

Suna inganta wake-waken Hausa da kayan kidan zamani.

Wannan na iya zama gaskiya ganin cewa yanzu yara kanana ko’ina ka je za ka gansu; ko ka ji suna ta faman rera wakokin fina-finan Hausa, su kuwa manya za ka ji suna sauraren wakokin, ko dai a gidaje; ko a shaguna; ko a cikin motoci.”

Marubucin har wa yau ya ambaci cewa, Gwamnati Jihar Kano ta kafa hukuma da ta dora wa alhakin tace fina-finai wadda ta haramta sa waka  da kida a cikin fina-finan amma har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, saboda sun saba wa al’adun Hausawa, a ga mace da namiji sun turke suna ta rera waka da ’yan tsalle-tsalle.

Idan muka lura da duk wadannan ka-ce-na-ce da ake ta gudanarwa a kan wadannan fina-finai. Za mu ga cewa, an tsangwami al’amuransu a dalilin wadannan abubuwa da ke biye:

Haduwar maza da mata

Lalata tarbiyyar yara da samari kamar yadda yake a cikin wasu fina-finai ta hanyar koyon sata ko fashi da makami da kuma shan miyagun kwayoyi.

Batanci ga addini, ta gurbata ayoyi da siffanta malaman addini da mummunar siffa.

Kawo bakin al’adu da rusa na al’umma da ke akwai

Mece ce mafita?

Dubi ga wannan al’amari, ya zama abin da aka sani a harshen addini da sunan AMMATIL BALWA. Ma’ana wani abu da ya game al’umma ya zama musiba wanda yake da wuya wani ya kubuta daga bala’insa. Ganin haka ne ya sa wadansu na ganin hana fina-finan kwata-kwata. Wadansu kuwa na ganin a tsabtace su. Daga cikin wadanda ke ganin a tsabtace su akwai Danjuma Katsina a cikin wata makala da ya rubuta a cikin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta 8/3/2002 mai taken: Bidiyon Kasuwar Kano! Martani ga Ibrahim Malumfashi. Shi wannan marubuci ya yi maganganu wadanda akwai abin dubawa a ciki. Daga cikin abin da ya rubuta akwai cewa, ko da an hana wadannan fina-finai a Arewa ana iya zuwa Kudu a sayo, kuma a shigo da su. Kai ana ma iya zuwa wasu kasashe a sayo, kuma a shigo da su. A dalilin haka yana ganin mafita ita ce a tsaya a gyara fina-finan na gida, yadda za su kori na waje marasa kyau. Daga cikin shawarwarin da ya bayar akwai:

Marubuta su  yiwo ca ga duk wani fim marar kyau, su kuma rika  fito-na-fito da duk wasu halaye munana da ya kamata masu shirya fina-finai su guji aikatawa.

Masu kallo su kaurace wa duk wani fim marar ma’ana da kuma kamfanin da ya shirya shi.

Gwammnatoci da masu kudi na iya fitowa da gidauniya wadda za a rika daukar nauyin yin fina-finai masu kyau da kuma yada su.

Idan muka dubi wadannan shawarwari na Danjuma, za mu ga suna da kyau, tun ma ba a ce shawara ta karshe ba. Domin abin da Hausawa ke cewa “Rashin uwa ke sa a yi uwar daki.” A nan da mawadatanmu da kuma gwamnatoci za su karbi wannan shawara a samar da fina-finai da suka dace da addininmu da al’adunmu, to, da ba a kallaci marasa kyau ba.

Akwai wata shawara da ake iya dubawa ga wadancan matsaloli da muka ambata a makon da ya gabata. Wannan kuwa ita ce samar da hukuma mai karfi da za ta fito da dokokin yin fim a kan dacewarsa da addininmu da kuma al’adunmu. Domin wannan ko a Turai akwai wadannan dokoki. Alal misali an fara kafa dokokin fim a kasar Amurka da aka shata sharuddan fitar da fim tun a 1915. Daga cikin sharuddan akwai, mutunci da dattaku da sanin ya kamata. Wannan an ce kuma su da kansu masu fitar da fim suka kafa wadannan dokoki kafin gwamnati ta kafa nata. Haka kuma su sun shata ga fina-finan da manya ke kallo da wadanda yara ke kallo da sauransu. Amma mu a nan a namu yanayi za mu yi abin da ya dace.

Kammalawa

Wannan kammalawa ta kasance ne a kan matsayar shari’a ga fina-finai. Abu ne sananne cewa fina-finai ba su bayyana ba a zamanin Manzon Allah (Tsira da Amincin Allah su tabbata gare shi), kuma ba su bayyana ba a zamanin sahabbai ba; haka kuma azamanin tabi’ai ballantana a ce sun yi magana a kansu. Amma da yake shari’ar Musulunci tsari ne na duniya gaba daya, kuma na har abada takan ba da dokoki da ka’idoji na gaba-daya domin su yi mana jagora. Ta  haka ne wani daga cikin mashahuran malamai na duniya ya wallafa littafinsa mai suna “Hukuncin Musulunci A Kan Kafofin Watsa Labarai.” Wannan malami shi ne Sheikh Abdullahi Nasiru Ulwana mutumin Siriya wanda ya rayu a kasar Sa’udiyya. Ya  nuna cewa idan wasan kwaikwayo ya kunshi abubuwa shida ya halatta a yi kuma a kallace shi. Ga abubuwan a takaice:

Kada a yi kwaikwayon wani ko wadansu mutane masu daraja da tsarki a zukatan al’umma kamar Annabawa da halifofi shiryayyu.

Kada ya kasance akwai alfasha, ko giya ko kuwa abubuwan gabatarwa na jima’i, kamar sumba da sauransu.

Kada ya zama akwai cudanyar maza da mata.

Ya kasance manufar wasan maslaha ce ta addini da ilimi da dabi’u nagari.

Kada wasan kwaikwayo ya zama manufarsa yi wa wani tsari na wajen aiki wanda yake manufarsa rusa al’umma.

Ya kasance marubuta wasan kwaikwayo mutane ne na kirki masu tsoron Allah.

Gyara kayanka ba zai zama sauke muraba ba. Wani sashi na wannan rubutu mun dauko daga shafin Intanet na Wikipedia.