Fitaccen malamin nan na addinin Islama, Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya assasa wata makaranta a cikin wani daji domin amfanar makiyaya wajen samun ilimin addini da na zamani.
Hakan dai na zuwa ne a yayin da Sheikh Gumi ya sha nanata cewa, samar da ababen more rayuwa a zamantakewar makiyaya zai taimaka wajen magance munanan akidu na tayar da zaune tsaye.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 15 a Sakkwato
- Budurwar da ta jira saurayinta shekara 16 ya fito a gidan yari
Gumi ya ce matsalar tsaro a Najeriya musamman ta’adar ’yan fashin daji ka iya zama tarihi muddin an yi musu wani tanadi na samun ilimi da sauran ababen morewa a zamantakewarsu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, makaranar da Sheikh Gumi ya sanya wa suna Cibiyar Sheikh Uthman Bin Fodio tana nan a birtalin kiwo na Kagarko da ke kusa da Kauyen Kohoto a Jihar Kaduna.
“Idan aka assasa irin wannan cibiya domin ilimantar da makiyaya a kowa lungu da sako na kasar to kuwa za a samu zaman lafiya a Najeriya.
“A maimakon makudan kudaden da gwamnati take kashewa a kan sojoji da kayan yaki, ya kamata a rika kashe kudaden domin makarantu da malamai.
“Ba sau daya ba tattauna da ’yan daban daji kuma sun bayyana aniyyarsu ta ajiye makamai su rungumi zaman lafiya muddin gwamnati za ta kula da ilimin ’ya’yansu da samar musu sauran ababen more rayuwa a zamantakewarsu.
“Abin da ya zaburar da ni na bude wannan cibiyar ilimi shi ne don magance matsalar rashin tsaro da muke fama da ita a kasar nan.
“Kasancewar kowane laifi akwai masu aikata shi kuma masu aikata laifuffukan suna da wani dalili, wanda kuma wannan dalili muke son ganin mun murkushe.
“Mun gano cewa ilimi shi ne zai magance duk wadannan matsaloli na rashin tsaro da muke fuskanta,” a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa, “muddin wadanda suke aikata miyagun laifuka a kasar aka yi musu tanadin hanyoyin da za su samu ilimi, to babu abin da zai sanya su rika aikata abin da a yanzu ake gani yana faruwa.
“Dole ne a tashi tsaye a ilimantar da su wanda hakan ya sanya muka assasa wannan cibiya domin ta zamanto abun koyi ga gwamnati a kowane matakinta da masu hannu da shuni da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.
“Ya kamata a hada kai wajen tunkarar bukatun makiyaya da ke rayuwa a cikin dazuka wanda ba su bukatar sai an kashe wasu makudan kudade kuma hakan zai taimaka gaya wajen samun zaman lafiya.
“Yanzu abin da muke da shi a kasa a wannan cibiya tana kunshe da azuzuwa guda shida da za a iya amfani da su a matakin karantarwa na Firamare da Sakandire a kowane lokaci.
“Ana iya karantarwa a kowane lokaci domin kuwa makarantar za ta riga gudana ne a tsawon sa’a 24 da ake da ita duk rana saboda yadda makiyaya ke fita kiwo tun daga misalin karfe 10 na safe kuma ba za su dawo ba har sai rana ta fadi.
“Saboda haka suna da sa’a biyu zuwa uku da za su iya daukar darasi kafin su fita kiwo, sannan kuma akwai fitilu da za mu sanya masu amfani da hasken rana saboda su samu damar yin bitar karatuttukansu idan dare ya yi.
“Idan aka assasa makamanciyar wannan cibiya ko’ina a fadin kasar nan, ’yan Najeriya za su zauna cikin aminci,” in ji Gumi.