✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Guguwa ta rusa gidaje da dama a Yobe

Al’ummar garin Girgir da ke Karamar Hukumar Jakusko ta jihar Yobe sun shiga damuwa bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da tsawa sun rushe…

Al’ummar garin Girgir da ke Karamar Hukumar Jakusko ta jihar Yobe sun shiga damuwa bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da tsawa sun rushe musu gidaje tare da lalata kadarori.

Wani mazaunin garin na Girgir, Abubakar Musa, ya ce ruwan sama mai karfi da tsawa da aka yi sun rusa gidajensu wadanda mafi yawansu ginin laka ne.

  1. Kotu ta umarci likitoci su koma bakin aiki nan take
  2. An kama masara da gero masu dauke da guba a Kano

Abubakar ya kara da cewa iska ta kware rufin kwanon wasu gidaje ta kuma katse hanyoyinsu na samun ruwan sha.

A cewarsa, asarar da suka yi ba za ta misaltu ba a halin yanzu, amma suna ci gaba da kokarin kididdige yawan abun da suka rasa.

Mutanen yankin sun nemi gwamnati da masu hannu da shuni da kuma daidaikun mutane su kawo musu dauki.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe, Dokta Muhammad Goje, ya ce suna tattaunawa da hukumomi masu ruwa da tsaki da suke aiki tare don ganin yadda za a taimaka wa mutanen yankin.