✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Guguwa ta hallaka mutum 23 a Amurka

Cikin mamatan har da kananan yara.

Mutum akalla 23 aka tabbatar sun mutu a sakamakon wata mahaukaciyar guguwa da ta tafka barna a jihohin Mississippi da Alabama da ke Kudancin Amurka.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta ce yanzu haka ana neman mutane 4 da suka bace bayan afkuwar ibtila’in.

Haka kuma, wasu gommai sun samu raunuka a bangare guda dubunnan iyalai sun fuskanci katsewar lantarki a Mississippi da Alabama da kuma Tennessee.

Shaidun gani da ido sun bayyana wa manema labarai cewa da tsakaddare ne kakkarfar iskar hade da tsawa ta afka wa yankin lokacin da ake tsaka da zabga ruwan sama.

Wannan lamari da ya haddasa asarar rayukan mutane 23 ya hada har da kananan yara hadi da kwashe rufin gidaje da dama tare da yin awon gaba da wasu.

Bayanai sun ce bayan afkuwar ibtila’in na tsakar dare anga yadda iskar ta wurgi da tarin ababen hawa zuwa wasu yankuna daban baya ga karya tarin bishiyoyi wadanda karfin iskar ya jijjigo su tun daga tushe.

Tashoshin Talabijin a jihar ta Mississipi sun hasko irin barnar da kakkarfar iskar ta yi wa garin.

Yanayin munin lamarin ya sa, hukumomi sun gargadi jama’a da su yi taka tsan-tsan a yayin da suke cewa, har yanzu akwai kalubalen da ake fuskanta mai barazana ga rayuwar al’umma a yankunan.

Ibtila’in ya tafka barna da kawo yanzu ba a iya tantance asarar da aka tafka daga guguwar iskar ta daren ranar Juma’ar da ta gabata ba.