’Yan sandan na binciken wani abin al’ajabi da ya faru da wata mata mai shekara 25 wadda ta yi ikirarin cewa ta haihu bayan samun juna biyu da awa daya, kuma wucewar iska ce ta samar mata da juna biyun.
Matar mai suna Siti Zainah wacce ake ta yada ta game da batun ta hanyar izgilanci, bayan ta ce wucewar guguwa ce ta sa ta samu juna biyu a ranar 10 ga watan Fabrairun da ya wuce.
- Gobara ta tashi a kusa da Masallacin Annabi na Madina
- Yadda aka kama wata mata da ke shayar da maciji nononta
- Wutar Lantarki: ’Yan Boko Haram sun sake jefa Maiduguri a duhu
Zainah ta ce, “Na haifi jaririya bayan awa daya da samun juna biyu.” A cewar kafofin labarai na kasar Indonesiya.
Mai jegon ta ce tana hutawa a gidansu da ke garin Cianjur, a Gundumar Java ta Yamma tare da danta na farko, sai ta ji iska ta shiga jikinta, bayan dan lokaci sai ta fara nakuda.
“Bayan Sallar Azahar, sai na kwanta kan cikina, jim kadan sai na ji iskar na saduwa da ni.
“Lokaci kadan sai cikina ya girma, sai ya ragu kamar yadda yake a baya, sannan ya sake girma,” inji ta.
Zainah ta yi zargin cewa, cikin nata ya fara girma ne kimanin minti 15, bayan ta gaza fahimtar abin da ke faruwa da giftawar iskar guguwar sannan ta fara jin ciwon ciki.
Daga nan ta fahimci ba daidai take ba, sai ta bukaci ’yan uwanta su kai ta cibiyar kiwon lafiya ta Cidaun da ke unguwar.
Bayan ganin likita, sai ya ce tana da jariri a mahaifarta, kuma lokacin haihuwar ya yi.
Na firgita —Mai jego
“Na firgita saboda lokaci guda na samu juna biyu, sannan na haihu,” inji ta.
Bayanan Zainah sun ba kowa mamaki inda wadansu ke yin izgilanci game da abin da ya faru da ita.
Hakan ya sa aka yi ta yada rahoton kamar wutar daji yayin da wadansu suka zo gidan don ganin mai jegon da jaririyarta.
’Yan sanda sun ziyarci gidan su Zainah don yi mata wasu tambayoyi game da samun juna biyun da ta yi, bayan da rahoton samun cikin nata ya ja hankalin kafafen labarai na kasar Indonesiya.
Shugaban Cibiyar Lafiya ta Cidaun mai suna Eman Sulaeman ya ce, bayanin Zainah kan samun juna biyunta abu ne ba mai yiwuwa ba a fannin likitanci, sai dai bai ce Zainah karya ta shirga ba.
Sai dai Eman Sulaeman ya ce, akwai yiwuwar cewa, hakan na iya faruwa ne a yanayin da ake kira, “Cryptic pregnancy,” inda mace za ta kasance dauke da juna biyu amma ba ta sani ba har zuwa lokacin haihuwa kafin ta gano haka.
Sulaeman ya kara da cewa, irin wannan haihuwar za ta iya faruwa ne sanadiyyar wasu halittu ko tarihin haihuwar da ake yi.
Abu mai dadin shi ne, wannan ba shi ne karon farko da ya taba faruwa a Indonesiya ba.
A bara an samu wata mai shekara 30 mai suna Heni Huraeni da rahoton haihuwarta ya dauki hankalin kafafen labaran kasar, saboda ikirarin cewa, ta haihu bayan awa daya da jin alamun samun juna biyu.