Yanzu haka an rufe makarantu da kasuwanni a Kananan Hukumomin Kaura da Jama’a da ke Kudancin Kaduna, saboda fargabar barkewar rikici.
Matakin dai ya biyo bayan hare-haren da aka kai a yankin Agban da ke Marabar Kagoro zuwa hanyar Gidan Waya da ke kan iyakokin kananan hukumomin.
- An sanya dokar hana fita ta sa’a 24 a Kudancin Kaduna
- EFCC ta bayar da belin tsohon Gwaman Anambra, Obiano
Rahotanni sun kuma ce yanzu haka mutane na can suna guduwa zuwa inda ’yan uwansu suka fi yawa, saboda kaucewa abin da zai iya biyo baya.
Hakan, ana zaton na da nasaba da kisan wani dan garin Kafanchan mai suna Dan-Asabe da aka yi da safiyar Litinin, a kan hanyarsa ta shiga Kafanchan daga Mariri, inda aka tare shi a Maraban Kagoro, aka kashe shi.
Da misalin karfe 9:00 na daren Lahadi ne wasu da ba a san ko su waye ba suka kai hari a yankin Kagoro da ke Karamar Hukumar Kaura.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton dai motocin jami’an tsaro ne ke ta karakaina a manyan titunan Kafanchan.
Lokacin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, don jin karin bayani bai amsa wayar wakilinmu ba.