✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gudaji Kazaure: Ina nan tare da Buhari, duk da na bar APC

Ya ce har yanzu shi cikakken mai biyayya ne ga Shugaba Buhari, duk kuwa da cewa ya bar APC

Dan Majalisar Wakilai, Muhammad Gudaji Kazure, ya ce har yanzu shi cikakken mai biyayya ne ga Shugaba Buhari, duk kuwa da cewa ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC.

Gudaji Kazarue, mai wakiltar Mazabar Kazaure/Yankwashi/Roni na Jihar Jigawa, ya ce babu abin da ya sa shi ficewa daga APC zuwa jam’iyyar ADC face abin da ya kira zaluncin da Gwamnan Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar, ya yi masa.

Dan majalisar wanda ya fadi zaben fidda gwanin neman komawa kujerarsa a karkashi APC, ya ce, “Tabbas na bar APC, amma ina mubaya’a ga Shugaba Muhammudu Buhari kuma.

“Gwamnana ya hana ni tikitin komawa kujereta a Majalisar Wailai, amma hakan ba abin da ya sauya, na koma jam’iyyar kuma jama’ata sun ba ni tabbacin samun nasara,” in ji shi.

Gudajei kazaure dai ya yi fice wurin goyon bayan Shugaba Buhari da kuma fitowa karara wajen sukar wasu tsare-tsaren gwamnatinsa.