✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Griezmaan ya sake komawa Atletico Madrid

Dan wasan ya koma Atletico Madrid a matsayin aro na shekara biyu.

Tsohon dan wasan gaban Atletico Madrid, Antoine Griezmaan ya sake komawa kungiyar, shekara biyu bayan ta sayar da shi ga Barcelona.

Griezmaan ya koma Atletico Madrid ne a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasanni ta 2022, tare da yiwuwar sayen sa kan Yuro miliyan 40.

Griezmaan ya amince ya sanya hannu a tsohuwar kungiyar tasa na tsawon shekara biyu, bayan gaza yin katabus a Barcelona wadda ta narka makudan kudi wajen sayen sa.

Tun a bara aka fara rade-radin dan wasan zai bar Barcelona, bayan ya gaza cim-ma abin da kungiyar take muradin samu daga wajensa.

Ko a farkon bude kasuwar cinikin ’yan wasa, Barcelona ta yi yunkurin sayar da Griezmaan don samun karin kudaden da za ta kulla sabuwar yarjejeniya tsakaninta da Messi, amma hakan ba ta samu ba.

Dan wasan na daukar makudan kudade a Barcelona amma ya gaza murza leda kamar yadda ya yi a Atletico Madrid.

Hakan ne ya sa a baya-bayan nan magoya bayan Barcelona suka fara yi masa ihu a duk lokacin da yake murza leda.