Jihar Gombe ce za ta wakilci jihohin Arewa maso Gabas a gasar wasannin ta kasa da za a gudanar daga ranar 20 ga Maris din bana a garin Benin.
Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Gombe, Malam Hamza Adamu Soye ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da wakilinmu bayan dawowarsu daga wasannin da suka fafata na Shiyyar Arewa maso Gabas a garin Maiduguri inda Gombe ta samu nasara a wasanni hudu cikin shida da ta shiga.
Hamza Adamu Soye, ya ce Gwamna Inuwa Yahaya, ya ba su duk tallafin da suka nema wanda hakan ya ba ’yan wasan kwarin gwiwa suka yi wasa har suka samu nasarar kaiwa gaci.
Shugaban ya ce sun samu nasara a wasan Kwallon Kwando da Kwallon Hannu da Kwallon Hannu na Yashi (Bich Bolleyball) na Mata inda suka zama zakarun da za su wakilci Arewa maso Gabas.
Hamza Soye, ya ce matsalar da suka samu a bangaren kwallon kafa ce inda aka ki yarda da tsarin da suka gindaya wanda hakan ne ya kai su ga rashin nasara.
Ya ce wasannin da za a fafata a garin Benin sun hada da wasan Ninkaya da Kokawar Gargajiya da ta zamani da wasan Tseren Keke wadanda ba a fafata gasar kansu ba a Maiduguri.
Malam Hamza Soye, ya ce ba su fuskanci wani kalubale ba a lokacin wasannin saboda ’yan wasansu sun sa jiki sun yi wasa sosai saboda sun samu karfin gwiwa daga Gwamna Inuwa Yahaya kafin a tafi wasan.
Ya ce Ministan Wasanni ya aiko wa Gwamna takarda kai-tsaye da ya sanya hannu cewa wasan na garin Benin zai gudana saboda yadda ’yan wasan Jihar Gombe suka samu nasara.
Ya kara da cewa a wasan da za su yi za su samar wa wadansu ’yan wasa sana’a domin a can ne kokarin da suka yi zai sa wasu kulob-kulob su dauke su su rika buga musu wasa.
Sai ya yi kira ga ’yan wasan cewa su kara himma don su sake daga martabar Jihar Gombe a idon duniya.