Kulob din Golden Academy Saminaka da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna ta lashe kofin da Kansilan mazabar Abadawa Alhaji Munkaila Bawa ya sanya bayan ya ci kulob din FC Formula 2-0.
An buga wasan karshen ne a filin wasa na Hayin Gada.
Da yake jawabi a lokacin da yake mika kofin ga Golden Academy, Kansilan mazabar Abadawa Alhaji Munkaila Bawa ya ce ya sanya wannan kofi ne don ya ba da gudunmuwarsa wajen bunkasa harkokin wasanni, don kuma ya dada hada kan matasan wannan yanki, sannan ya bukaci matasan yanki su rungumi harkar wasanni, domin hanya ce ta samun kudi.
Kocin kulob din Golden Academy Saminaka Abdulganiyu Abdul’aziz ya mika godiyarsa ga Allah kan nasara da suka samu na cinye wannan kofi.
kulob 16 wadanda suka fito daga sassan karamar Hukumar ta Lere ne suka fafata a gasar, an raba wa kungiyoyin kayayyakin wasanni daban-daban.
Golden Academy ta lashe kofi a Saminaka
Kulob din Golden Academy Saminaka da ke karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna ta lashe kofin da Kansilan mazabar Abadawa Alhaji Munkaila Bawa ya sanya…