✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Golan Najeriya Enyeama ya zama Gwarzon dan kwallon Afirka a Faransa

bincent Enyeamba golan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka  a gasar rukunin Faransa da aka fi…

Vincent Enyeamabincent Enyeamba golan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ne aka zaba a matsayin Gwarzon dan kwallon Afirka  a gasar rukunin Faransa da aka fi sani da Ligue 1.
Gasar wacce ake wa lakabi da Marc-bibien Foe ana gudanar da ita ne ga ’yan kwallon da suka fito daga Nahiyar Afirka wadanda ke buga kwallo a Faransa a duk shekara.
Golan, wanda yake buga wa kulob din Lille na Faransa wasa, ya doke abokan takarsa dan asalin Kwaddebuwa Serbge Aurier ne da ke buga wa kulob din Toulouse FC da kuma dan Kamaru Henri Bedimo da ke wasa a kulob din Olympikue Lyonnais. daukacin marubuta labarin wasanni da ke Faransa ne suke gudanar da zaben.
Enyeama, dan kimanin shekara 31 ya samu nasarar lashe gasar ce bayan ya yi wasanni 11 ba tare da kwallo daya ta shiga ragarsa ba ma’ana ya yi mintuna 1,062 ba tare da shigar kwallo ragarsa a gasar rukunin ba.
Kawo yanzu Enyeamba ya buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles wasa sau 82 kuma ya taimaka wa Najeriya wajen lashe gasar cin kofin Afirka da aka yi a Afirka ta Kudu a  bara kuma shi aka sa ran zai kama wa kungiyar wasa a gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a wata mai zuwa.