✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a yi jana’izar golan Afirka ta Kudu

A gobe Asabar ne ake sa ran za a yi jana’izar golan kulob din Orlando Pirates da kuma kungiyar kwallon kafa ta Bafana-Bafana da ke…

A gobe Asabar ne ake sa ran za a yi jana’izar golan kulob din Orlando Pirates da kuma kungiyar kwallon kafa ta Bafana-Bafana da ke Afirka ta Kudu mai suna Premier Senzo bayan da wadansu ’yan bindiga suka kashe shi a gidansa a karshen makon jiya.

Za a yi jana’izar ce a kauyensu mai suna Umlazi da ke Durban a Afirka ta Kudu.
A ranar Litinin da ta gabata ne, shugaban kulob din Orlando Pirates tare da mukarrabansa suka kai ziyarar jaje gidan iyalan marigayin watau golansu da wadansu wadanda har yanzu ba a gano ba suka kashe shi a gidansa al’amarin da ya janyo tofin Allah-tsine a daukacin kasar.
Shugaban ya ce ya yanke shawarar zuwa gidan iyalan mamacin ne don yi musu ta’aziyya saboda ya dauki marigayin tamkar dansa musamman ganin tun yana karami ya fara yi wa kulob din na Orlando Pirates wasa.