✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara gasar cin kofin duniya a Chile

A gobe Asabar 17 ga Oktoba 2015 ne ake sa ran za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da…

A gobe Asabar 17 ga Oktoba 2015 ne ake sa ran za a fara gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na ’yan kasa da shekara 17 a kasar Chile da ke Kudancin Amurka.
kasashe 24 ne daga sassan duniya  za su fafata a gasar don neman zakaran da zai lashe kofin.  Najerriya ce mai rike da kofin a halin yanzu bayan ta lashe wanda ya gudana a shekarar 2013 a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). Haka kuma Najeriya ta samu nasarar lashe gasar har sau hudu a shekarar 1985 da 1993 da 2007 da kuma a 2013.  Sannan kasashe hudu da suka fito daga Nahiyar Afirka ne  za su fafata a gasar da suka hada da Najeriya da Mali da Afirka ta Kudu da kuma Guinea.
A wasannin da za su gudana a a gobe Asabar  sun hada da wanda Ingila za ta kece raini da Guinea, Najeriya kuma ta hadu da Amurka sai wasan Brazil da Korea Republic yayin da mai masaukin baki Chile za ta kara da Kuroshiya.
Sai jibi Lahadi Beljiyam da za kara da Mali sai wasa a tsakanin Austireliya da Jamus sai Honduras da Ekwado sai kuma wasan Meziko da Ajantina.
Gasar za ta gudana ne a tsakanin ranakun 17 ga watan nan zuwa 8 ga watan gobe na Nuwamba watau a tsakanin makwanni uku.