✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobe za a fara gasar cin kofin Afirka

A gobe Asabar 17 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a fara gasar cin kofin Afirka karo na 30 a…

A gobe Asabar 17 ga wannan wata da muke ciki ne ake sa ran za a fara gasar cin kofin Afirka karo na 30 a Ekuatorial Guinea.

kasashe 16 ne za su fafata a gasar, sai dai Najeriya ba ta kasance cikin wadanda za a dama da su a gasar ba.
Gasar za ta gudana ce a tsakanin ranakun 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun 2015.
kasashen da za su fafata a gasar sun hada da mai masaukin baki Ekuatorial Guinea da Afirka ta Kudu da Congo da Aljeriya da Mali da Gabon da Burkina Faso da Kamaru da Kwaddebuwa da Dimokuradiyyar Kongo da Ghana. Sauran kasashen sun hada da Guinea da Cape berde da Zambiya da Tunisiya da kuma Senegal.
Najeriya ce ta lashe gasar a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu amma abin takaici ta kasa hayewa gasar ta bana bayan Kongo ta yi mata kancal a yayin gasar neman hayewa gasar.
Masoya kwallon kafa a ciki da wajen kasar nan tuni suka nuna bacin ransu a kan rashin halartar kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles gasar.