Hukumar shirya kwallon kafa ta Tunisiya ta amince da yin wasan sada zumunta da kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 23 ta Najeriya watau (Nigeria’s Under 23) a gobe Asabar a can Tunisiya. Sannan ana sa ran kungiyar U-23 din za ta sake yin wasan sada zumunta da takwararta ta Aljeriya a ranar Laraba mai zuwa.
Bayanin haka na kunshe ne a wata takardar amincewa da wasan da Hukumar FA ta Tunisiya ta aikowa Najeriya a ranar Litinin da ta gabata.
Tuni kocin Tunisiya mai suna Nizar Khanfir ya fitar da jerin sunayen ’yan kwallon da za su fafata da Najeriya a lokacin wasan. Haka shi ma kocin Najeriya Samson Siasia ya fitar da nasa sunayen ’yan kwallon da zai yi amfani da su a wasan.
Haka kuma Siasia ya fitar da jerin ’yan kwallon da za su buga wa Najeriya a gasar sada zumunta ta kasashe shida da za ta gudana a Abuja a tsakanin ranakun 24 ga Fabrairu zuwa 11 ga watan Maris a Abuja.
Ana gudanar da gasar kasashe shida ne daga yankin Afirka a duk bayan shekara biyu kuma wannan karon gasar za ta gudana ne a Abuja.