A gobe Asabar kocin Chelsea Jose Mourinho zai san matsayinsa bayan kulob din ya hadu da na Liberpool a gasar rukunin firimiya na Ingila. Akwai yiwuwar kulob din ya kori kocin muddin ya sha kashi a wasan gobe.
Idan za a tuna a ranar Lahadn da ta wuce ne kulob din ya sha kashi a wajen West Ham United da ci 2-1 a gasar firimiyar Ingila da hakan ya sa kawo yanzu kulob din ya samu rashin nasara a wasanni biyar a gasar ta bana. s Don haka idan Liberpool ta sake doke kulob din a gobe Asabar to babu makawa kujerar kocin ta cigaba da yin rawa.
Abin mamaki shi ne kulob din Chelsea ne ke rike da kambun gasar firimiya ta Ingila bayan ya lashe kofin a bara, amma tun da aka fara gasar a bana sai kulob din ya shiga tangal-tangal.
Ya zuwa makon jiya dai mahukunta kulob din Chelsea sun nuna goyon bayansu ga kocin duk da irin kalubalen yake fuskanta amma ganin yadda kulob din yake ci gaba da samun rashin nasara musamman a wasan da kulob din ya yi da na Stoke City a ranar Talatar da ta wuce a kofin Carling ta sa wasu magoya bayan kulob din da wadansu daga cikin ’yan kwallon suke ganin da wuya kocin ya kai labari muddin kulob din Liberpool ya doke shi a wasan gobe.