Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana kaduwarsa game da gobarar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane da dama Jihar da safiyar Laraba.
Hukumar Kiyaye Haddura ta kasa (FRSC) reshen Jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutum 23 a gobarar tana mai cewa hudu daga cikin mamatan sun kone kurmus.
A sakon jajen da Sakataren Watsa Labaransa, Onogwu Mohammed ya fitar, Yahaya Bello ya ce iftila’in shi ne babban asarar da ta samu jihar a yanzu.
Tun da farko wasu rahotanni sun ce mutum 40 ne suka mutu bayan tankar dakon man ta kama da wuta a yankin Felele da ke garin Lokoja na Jihar Kogi a safiyar Laraba.
- Masu manyan motoci sun janye yajin aiki
- Abin da ya sa aka rufe Gidan abincin N30
- Yadda aka yi addu’ar ukun Sarkin Zazzau
Daga cikin mutanen da suka hallaka a gobarar da ta tashi bayan motar ta yi bindiga akwai mutum bakwai ‘yan gida daya da suka hada da wasu ma’aurata da ‘ya’yansu biyar.
Gobarar ta faru ne bayan birkin motar man ta tsinke, wanda hakan ya sa moatar kwacewa daura da kofar shiga Kwalejin Fasaha ta Jihar Kogi da ke garin Lokoja.
Rahotanni sun ce mamatan da abin ya rutsa da su sun hada da daliban kwalejen ciki har da kananan yara.
Mataimakin gwamnan jihar Edward Onoja da ma mai dakin Gwamna Yahaya Bello sun isa wurin da abin ya faru, inda ta ce wasu fusatattun mata sun tare hanyar.