Rahotanni na bayyana cewa, mutum uku ne suka rasu a safiyar yau Talata lokacin da wata tankar man fetur ta yi gobara a rukunin gidajen gwamnati da ke phase 4 axis a Fatakwal babban birnin jihar Ribas.
Wani ganau ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:00 na tsakar dare lokacin da wata tankar man fetur ta kama da wuta, wanda hakan ya sa wasu gidajem suka yi gobara.
Cikakken rahoton na nan tafe.