✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobarar tankar mai ta jikkata mutum 64 a Kano

Laifin wannan gobara na mahukuntan gidan man ne.

Kimanin mutum 64 ne suka samu raunuka daban-daban sakamakon gobarar da ta auku yayin da wata tankar mai ta fashe cikin a Jihar Kano da yammacin ranar Asabar.

Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne yayin da tankar ke sauke man fetur a Gidan Mai na Al-Hisan da ke Layin Ali Gusau a Unguwar Sharada.

Daga cikin wadanda gobarar ta ritsa da su akwai Ma’aikatan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano da suka kawo dauki bayan amsa kiran neman agajin gaggawa.

Babu asarar rai ko daya da aka samu, inda a halin yanzu wadanda suka jikkata ke samun kulawa a Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed da ke kwaryar birnin Kano.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara na Kano, Saminu Yusuf Abdullahi wanda ya inganta rahoton, ya ce jami’ansu takwas na daga cikin mutum 64 da suka jikkata.

Rahotanni sun bayyana cewa, Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, Garba Shehu, ya jingina alhakin tashin gobarar a kan sakacin mahukuntan gidan man.

A cewarsa, “Kowa ya sani doka ta haramta sauke mai da tsakar rana musamman a irin wannan yanayi da Kano ke ciki na matsanancin zafi, wanda kuma hakan ne ya yi sanadiyyar tashin gobarar.”