✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobarar Monday Market: Buhari ya ba da umarnin tallafa wa ’yan kasuwa

Buhari ya nuna alhininsa dangane da gobarar kasuwar Monday Market

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da su yi aiki tare wajen tallafa wa wadanda gobara ta shafa a kasuwar Monday Market da ke Maiduguri, Jihar Borno.

Umarnin na kunshe ne cikin sanarwar da Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya fitar ranar Lahadi.

Buhari ya yaba da daukin gaggawar da gwamna jihar, Farfesa Babagana Zulum ya kai wajen kashe gobarar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da a kula da yadda ake amfani da wuta musamman a lokutan iska da zafi masu barazanar haifar da gobara a gida da daji.

Haka nan, Shugaba Buhari ya bukaci hukumomin kwana-kwana a matakin tarayya da jihohi da su matsa kaimi tare da samar da ingantattun matakai dangane da ayyukansu.

A karshe, shugaban ya nuna alhininsa tare da jajanta wa duka wadanda gobarar ta shafa.