Gwamnan Jihar Kano da wasu ’yan kasuwa a jihar sun ba da tallafin miliyan 20 don taimaka wa wanda iftila’in gobara ya shafa a jihar Katsina.
Ganduje tare da kwamiti na musamman sun ziyarci jihar Katsina, game da asarar da jihar ta yi a gobarar da ta cinye dukiyoyi da dama a Babbar Kasuwar Katsina.
- Yau za a ci gaba da gasar cin kofin zakarun Turai
- ’Yan bindiga sun kashe mutu 8 sun sace 28 a Kaduna
- ‘Tun ina shekara bakwai mahaifina yake kwanciya da ni’
- Buhari ya nada sabon Shugaban ’Yan sandan Najeriya
“Mun zo ne tare da Kwamitin ’yan kasuwa don wanda suka taba samun kansu cikin irin wannan hali a kasuwar Sabon Gari, don jajanta muku game da gobarar da ta faru a watan da ya gabata.
“Muna addu’ar kiyaye faruwar hakan a gaba. Sannan muna jan hankalin Gwamna Masari da ya kafa kwamiti don bincikar musabbabin tashin gobarar,” a cewar Ganduje.
Ganduje ya ce Kano da Katsina jihohi ne da suka dade suna tsintar kansu cikin irin wannan hali, don haka ya ce tallafin miliyan 20 zai rage radadi ga wanda abun ya shafa.
Da yake nasa jawabin, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce jihohin biyun, ba wai iyakoki kadai suka hada ba, suna da alaka mai tarin shekaru.
Sannan ya gode wa Ganduje da Kwamitin ’yan kasuwar bisa tallafin da suka bayar.
Kazalika, ya ce tallafin zai taimaka gaya wajen rage radadi ga wanda gobarar ta yi wa barna.