Wata gobara ta kone buhunan amfanin gona 1,900 na miliyoyin naira da ta tashi a babbar kasuwar hatsin nan da ke Karamar Hukumar Gombi ta Jihar Adamawa.
Gobarar wacce ta kone shaguna 19 a kasuwar da Yammacin ranar Alhamis, ana zargin ta tashi ne a dalilin jefar da ragowar karan sigari da ke ci da wuta da wani wanda ba a san ko wane ne ba ya yi a cikin dan jejin da ke bayan shagunan.
- Ana zargin wata mata da satar talabijin a Gombe
- Gwamnati za ta bai wa ma’aikata tallafin rage raɗaɗi a Yobe
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda mataimakinsa, Farfesa Kaletapwa Farauta ya wakilta, ya ziyarci fadar Dagacin Gombi, Usman Ibrahim Sarkinfada domin jajanta masa da kuma talakawansa.
Gwamnan ya yi addu’ar Allah Ya kawar da fitina da fatan kada irin wannan bala’in ya sake aukuwa a nan gaba.
Dagacin ya bayyana farin cikinsa ga Gwamnatin Jihar Adamawa da ta nuna damuwarta dangane da wannan mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki.
A ziyarar da ya kai kasuwar da lamarin ya faru, Gwamna Fintiri ya bayyana asarar da aka yi a matsayin babbar musiba, yana mai cewa hakan wani mummunan koma baya ne ga tattalin arzikin Gombi da Jihar Adamawa da ma Najeriya baki daya.
Ya kuma gargadi mazauna da su rika taka-tsan-tsan wajen kone dazukan da ke kusa da wurare na zamantakewa ko kasuwanci, musamman a irin wannan lokaci na sanyi.
Kazalika, Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamna Fintiri a yayin ziyarar ya duba wasu ayyukan da ake gudanarwa a kasuwar.