✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ƙone ofishin INEC a Sakkwato

“Rahoto na farko daga ofishinmu na jihar ya nuna cewa an samu ƙaruwar wutar lantarki kafin faruwar lamarin,”

Hukumar Zaɓe Mai ta Ƙasa (INEC) ta ce ofishinta na Ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato ya ƙone ƙurmus, inda  gobarar ta lalata akwatunan zaɓe da sauran kayayyaki.

Mista Sam Olumekun, kwamishinan Hukumar INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata sanarwa.

A cewarsa, a taron Hukumar INEC na mako-mako da aka saba gudanarwa a ranar Alhamis, hukumar ta lura da wani mummunan lamari na tashin gobara a ofishin ƙaramar hukumar Gwadabawa da ke Jihar Sakkwato, kamar yadda sakatariyar gudanarwa mai kula da ofishin jihar, Hauwa Aliyu Kangiwa ta ruwaito.

Ya ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Talata 11 ga watan Fabrairun 2025.

“Duk ginin ofishin ya lalace. Kayayyakin da suka lalace sun haɗa da tebura da kujeru da kayan aiki da kayan zaɓe da ake iya ɗauka, daga cikinsu akwai akwatunan zaɓe 558, rumfar kaɗa ƙuri’a 186, jakunkuna 186 na zaɓe da kuma kayayyakin da suka haɗa da manyan tankunan ruwa guda 12 (litta 1,000), tabarmin barci 400 da bokitan robobi 300.

“Rahoto na farko daga ofishinmu na jihar ya nuna cewa an samu ƙaruwar wutar lantarki kafin faruwar lamarin,” in ji Olumekun.