✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta ƙone kasuwa a Kwara

Wata gobara da ta tashi a kasuwar Ita Amodu da ke kan titin Old Yidi a Jihar Kwara, ta lalata dukiyar miliyoyin kuɗi.

Wata gobara da ta tashi a kasuwar Ita Amodu da ke kan titin Old Yidi a Jihar Kwara, ta lalata dukiyar miliyoyin kuɗi.

Gobarar, wadda ta tashi a ranar Talata, ta jawo wa ‘yan kasuwar da ke sayar da katifa, darduma, da sauran kayayyaki asara mai yawan gaske.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Hassan Adekunle, ya bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga mota da ke ɗauke da katifu.

Motar ta kama da wuta sannan wutar ta bazu zuwa gine-ginen da ke kusa da ita.

Ya ce, “Wutar ta lalata motar kuma ta shafi wani gini da ke ɗauke da ɗakuna 47 da shaguna 19. Bayan kai agajin gaggawa mun yi nasarar daƙile wutar daga kama ɗakuna 31 da shaguna 12, yayin da ɗakuna 16 da shaguna bakwai suka ƙone ƙurmus.”

Ya bayyana cewar bincike ya nuna motar, wadda aka ɗora wa kaya fiye da ƙima, ta yi karo da wayar wutar lantarki wanda hakan ya sa wuta ta tashi.

Tashin wutar ya haddasa tashi gobarar, wanda ta bazu cikin sauri tare da kama kayayyaki.

Lamarin ya ƙara ta’azzara lokacin da wani janareta da ke kusa da motar ya yi bindiga, wanda ya sa gobarar ta bazu zuwa shaguna da ɗakunan da ke kusa.

Adekunle, ya gode wa Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, ’yan sanda, da kafafen yaɗa labarai kan gudunmawar da suka bayar wajen shawo kan gobarar.

Ya ce ’yan sanda sun kare ma’aikatan kashe gobara daga ɓata-gari yayin da suke aikin kashe wutar.