✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi ta’adi a kasuwar ’Yan Katako a Zariya

A iya shagonmu, mun tafka asara ta kimanin naira miliyan 18 sakamakon wannan gobara.

Gobara ta tashi a kasuwar ‘Yan Katako ta Sabon Gari a birnin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da daddare zuwa wayewar garin Laraba.

Wani mai shago a kasuwar Idris Mai Kusa ya bayyana cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe biyu na dare.

Babu tabbaci kan kan me ya jawo gobarar sai dai ana zargin wutar lantarki ce ta haddasa ta.

“An kira ni da misalin karfe biyun dare aka ce mani an kawo wuta sai kawai wani turken wuta ya yi tartsatsi a kusa da wuraren da shagunanmu suke, daga nan ne wutar ta tashi,” a cewarsa.

“Ko lokacin da na kira kasuwa domin na ji wane hali ake ciki, shagunanmu sun riga sun kone,” in ji Idris.

Ya bayyana cewa motar kashe gobara guda daya ta je kasuwar domin kashe wutar amma lamarin ya gagare ta saboda wasu matsaloli.

Ya bayyana cewa a halin yanzu babu wani mutum da zai iya kididdige yawan asarar da aka tafka sakamakon wannan gobarar, amma ya ce akwai shaguna da dama da suka kone.

“Kayan da ke cikin shagonmu kadai wadanda suka kone a iya lissafi za su iya kai na miliyan 18, wasu shagunan ma sun fi mu asara,” in ji Idris

Ya bayyana cewa bisa kiyasi shaguna sama da 100 sun kone sakamakon wannan gobarar.

Shi ma Sani Yusuf Dace wanda a kasuwar ta ‘Yan Katako yake ya bayyana cewa sun tafka asarar da ba ta misaltuwa.

“Allah ne Ya jarabce mu, daga Allah ne kuma mun bar masa, Allah Ya musanya mana da alkhairi,” in ji Sani.

Ya bayyana cewa lissafin iya dukiyar da aka yi asara sai an zauna saboda a cewarsa asarar tana da yawa.

Shi ma Rabi’u na Alhaji Ahmadu da ke kasuwar ya shaida cewa sun yi asara ta miliyoyi sakamakon wannan gobara.

Ya bayyana cewa wannan kaddara ce da Allah Ya aiko musu kuma sun dauki kaddarar.

Kawo yanzu dai hukumomi ba su ce komai ba tukunna dangane da wannan gobara.

TRT