Wata gobara da ta tashi da a yau Laraba a shagunan Kasuwar Idumota ta Jihar Legas, ta lalata dukiya ta miliyoyin nairori.
Gobarar ta shafi wasu gine-gine guda 3 ne, ciki har da wasu benaye masu hawa bibiyu da wani bene mai hawa ɗaya da ya ruguje a dalilin zafin wuta.
Bayanai sun ce an samu rushewar ginin ne a ɓangaren kasuwar da ya fi shahara da kasuwancin tufafi da takalma da jakunkuna.
- An ayyana Tukur Mamu da wasu 14 a matsayin masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya
- Kotu Ta Daure Barawon Alqur’ani Watanni 15 A Abuja
Tuni dai jami’an hukumar kwana-kwana da ba da agajin gaggawa ta Jihar Legas da sauran hukumomin ba da agaji suka isa wurin da lamarin ya faru inda suka ƙaddamar da aikin kashe gobarar.
A cewar Shugabar Hukumar Kwana-Kwana ta Jihar Legas, Margaret Adeseye, cibiyoyin kashe gobara na unguwannin Ebute Elefun da Ilupeju da Alausa sun tura jami’ai da kayan aiki domin taimakawa wajen shawo kan gobarar wacce tuni aka ƙaddamar da yaki da ita.
Har yanzu dai ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma an kaddamar da bincike akan hakan.
Haka kuma, ba a kai ga tantance asarar rai ko jikkata ba a sakamakon gobarar da ta auku a yankin Dosumo.
Adeseye ta bukaci mazauna yankin su bai wa jami’an ba da agajin gaggawa haɗin kai tare da kaucewa wurin domin kiyaye lafiyarsu.
Kazalika, Ko’odinetan hukumar NEMA a shiyyar Kudu-maso-Yamma, Ibrahim Farinloye, ya ce ma’aikatan agajin na fuskantar kalubale matuƙa dangane da karancin ruwa.