✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi ajalin yara 3, ta lalata dukiya a Yobe

Binciken da SEMA ta gudanar ya nuna yadda aka yi asarar dukiya kama daga kan gidaje, kayan abinci da sauransu.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA), ta ce ta samu rahoton mutuwar yara uku a wata gobara da ta tashi a garin Nguru na jihar.

Yayin da aka shiga yanayin sanyi, hukumar ta gargadi jama’ar jihar da yin taka tsan-tsan wajen amfani da wuta, da sauran na’urorin lantarki.

“SEMA na son yin amfani da wannan kafa wajen yin kira ga shugabannin al’umma da  magidanta da su yi taka-tsan-tsan a wannan lokaci, ta hanyar tabbatar da cewa an kashe duk na’urorin lantarki idan ba a amfani da su ba, a kashe itacen wuta yadda ya kamata bayan an kammala amfani da su.”

Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa ta shafinta na Facebook ranar Alhamis.

SEMA ta kuma bayyana cewa ta samu rahoton afkuwar gobara a kananan hukumomin Damaturu da Fune a tsakanin ranakun 28, 30 ga Disamba, 2022 da kuma 4 ga Janairu, 2023.

Binciken da SEMA ta gudanar ya nuna yadda aka yi asarar dukiya kama daga kan gidaje, kayan abinci da sauransu.

Hukumar ta ce tana kokarin tallafa wa wadanda lamarin ya shafa don rage musu radadin halin da suke ciki.