Wata gobara da ta tashi a sashen bada kulawa ta musamman a wani asibitin da ke Bagadaza, babban kasar Iraki, ta yi ajalin gomman masu fama da cutar Coronavirus.
Shafin Sky News ya ruwaito cewa, gobarar wacce ta tashi a asibitin Ibn al-Khatib da ke yankin gadar Diyala, ta yi kashe akalle mutum 27 tare da jikkata wasu mutum 46, lamarin da ya sanya a kai mayar da marasa lafiya kimanin 90 zuwa wasu asibitocin.
- Ramadan: Matasan Yobe sun tallafa wa ’yan gudun hijira
- Harin Geidam: Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 21
Gobarar ta tashi ne a sakamakon fashewar tukunyar iskar gas mai dauke da sunadarin oxygen da ke taimakawa marasa lafiya masu bukatar karin iskar numfashi.
Wani babban jami’in hukumar tsaro ta farin kaya, ya tuni aka kashe gobarar wacce ta tashi a daren jiya, inda galibi marasa lafiyar sun mutu a sakamakon cire musu iskar da suke shaka yayin da ke kokarin ceton rayukansu.
A safiyar Lahadi ce Firaminisa Mustafa al-Kadhimi ya yi kira da a fadada bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.
Kimanin mutum 1,025,288 ne suka kamu da cutar Coronavirus a kasar Iraqi, inda tuni mutum 15,217 sun riga mu gidan gaskiya kamar yadda Ma’aikatar Lafiyar Kasar ta bayyana.
Alkaluma sun nuna cewa ana samu akalla mutum dubu takwas sabbin kamuwa da cutar duk rana a kasar, duk da yadda gwamnati ke rokon al’umma su karbi rigakafinta, sai dai mutanen kasar ba su amince da rigakafin ba.