✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta yi ajalin jaririya a Binuwai

Mahaifiyar jaririyar ta je makaranta ta bar ta a gida lokacin da wutar ta tashi.

Wata jaririya ’yar wata uku ta gamu da ajalinta a wata gobara da ta tashi a yankin Awe da ke garin Makurdi a Jihar Binuwai.
Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru a kan idonsa ya ce ba a san abin da ya haddasa gobarar ba da safiyar ranar Litinin.
Wakiliyarmu ta samu damar ziyartar inda gobarar ta tashi a ranar Laraba, inda ta gane wa idonta yadda gobarar ta cinye dakuna biyu a gidan da wutar ta tashi.
Wani makwabcin gidan ya ce gobarar ta dauki tsawon lokaci kafin ta mutu, saboda rashin samun dauki daga hukumar kashe gobara ta jihar.
Mahaifiyar jaririyar mai suna Hamida Abdul, ta bayyana cewa ta je makaranta lokacin da wutar ta tashi, kuma a lokacin ta bar jaririyar a hannun makwabciyarta.
“Bana gida lokacin da al’amarin ya faru. Na je makaranta kamar yadda na saba kullum. Na yi mata wanka sannan na mika wa makwabciyata ajiyar ta kafin na dawo.
“Ina makaranta aka kira ni cewa wuta ta kama gidanmu. Kuma babu wanda ya san jaririyata na cikin gidan. Nakan bar ta a gida na je makaranta har na dawo. Lokacin da na dawo wutar ta gama cinye kusan komai.
Mahaifiyar ta yi wa Allah godiya kan iftila’in da ya same ta, da kuma tsira da danta mai shekara biyu ya yi a lokacin gobarar.
Wakiliyarmu ta yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, kan lamarin amma ba ta amsa wayarta ba.