✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gobara ta yi ajalin almajirai 17 a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewar gobarar ta tashi ne sakamakon wasu itatuwa da aka tara.

Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17.

Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba.

Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci.

Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar.

Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye.

Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali, a cikin ɗakin karatu.

“Akwai kusan almajirai kusan 100 a cikin gidan. Bayan da aka fitar da su, sai aka ɗauka babu kowa a ciki.

“Amma bayan gobarar ta lafa, sai aka dawo aka ga sassan jikin wasu kamar ƙafafu, hannaye, da kuma gawarwakin waɗanda suka rasu bayan sun ƙone ƙurmus.”

An yi jana’izar waɗanda suka rasu a ranar Laraba.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda, Kwamared Mannir Muazu Haidara, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa wajen da lamarin ya faru domin samun ƙarin bayani.