Gobara ta tashi a kasuwar Ajao da ke jihar Legas, ta kuma kama wasu gine-gine masu makwabtaka da kasuwar, lamarin da ya sa mazauna tserewa daga gidajensu.
Kakakin Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) Nosa Okunbor, ya ce LASEMA da Hukumar Kwana-kwana ta jihar da ‘yan sanda na kokarin kashe gobarar.
- Gobara ta lakume rumfunan kasuwa a Legas
- Yadda gobara ta yi barna a babbar kasuwar jihar Edo
- Hotuna: Gobarar tankar mai a kan gada ta haddasa cunkoso na awanni a hanyar Legas
“Gobarar ta fara da misalin 1.00 na dare amma mun riga mun iso wurin. Mun samu labari cewa ta faro ne daga wani shago, ta watsu zuwa sauran kasuwar da gine-ginen da ke makwabtaka da ita”, inji shi.
Amma ya ce babu tabbacin asarar rai kuma ba su kai ga tabbatar da iya barnar da wutar ta yi ba, duk da cewa an tafka asarar dukiya.
A iya cewa rahoton farko ke nan da aka samu na gobara a kasuwa a watan Yuli, bayan wadanda aka samu a wasu kasuwanni a cikin watan da ya gabata a wasu sannan Najeriya.