Gobara ta kone fitacciyar tashar mota ta NTA da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato.
Mista Matthew Edogbonya, kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya a Jihar Filato, bai samu damar amsa waya ba.
- Gwamnati za ta lalata bindigogi 3,000 da ta kwato a hannun ’yan ta’adda
- Gwamnan Adamawa: Kotu ta tabbatar da takarar Binani
Amma wani babban jami’in hukumar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da faruwar lamarin a Jos.
“Kakaki da sauran manyan jami’an hukumarmu suna wurin da gobarar ta tashi sai dai har yanzu ba su ce komai ba.
“Ba za mu iya cewa ga musabbabin faruwar gobarar ba, amma an tura mutanenmu wurin domin kashe ta.
“A halin yanzu, ba za mu iya cewa ga adadin abubuwan da suka salwanta ba.
“Abin da muka fi damuwa da shi a yanzu shi ne kashe gobarar saboda kada ta lalata dukiya ko salwantar rayukan mutane,” in ji shi.
NAN ta ruwaito cewa tashar motar na daura da gidan talabijin na NTA da ke Jos, wanda ke kan hanyar Yakubu Gowon, Jos.