Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar ranar Talata ta kone wani sashe na Shalakwatar Sojojin Kasa ta Najeriya dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta kama ne da misalin karfe 10:15 na safe sakamakon wata tangardar wutar lantarki.
- Iyayen Daliban Jangebe na rige-rigen tafiya da su gida
- Alluran rigakafin COVID-19 na Najeriya sun iso
Kakakin Rundunar Sojin Kasa, Birgediya Janar Mohammed Yerima ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce wane sashen na ginin shalkwatar ya kama da wuta ne sakamakon wata kwaskwarima da aka yi a ginin, wacce kuma ta hada da gyaran wutar lantarki.
Sai dai kakakin ya ce tuni Sashen Kashe Gobara na Rundunar ya sami nasarar kashe gobarar.
Ya kuma ce ba a sami asarar rai ko da guda daya ba kuma tuni al’amura sun koma kamar yadda suke a baya.
“Gobarar ta samo asali ne daga wasu gyare-gyare ne da ake yi a shalkwatar, amma an kashe wutar kuma babu asarar rai ko guda daya,” inji Yerima.