’Yan Najeriya da ba a san iya yawansu ba sun rasa matsuguninsu, bayan gobara ta tashi a sansanin gudun hijirar da suka samu mafaka a Jamhuriyar Nijar.
Gobarar ta lakume daruruwa wuraren kwana a sansanin ’yan gudun hirija na Gigime, inda aka tsugunar da ’yan Najeriya da suka sallaka zuwa kasar Nijar.
Wata majiya ta ce sama da ’yan gudun hijira 400 ne gobarar a kona wurin kwanansu, baya ga kayan abinci da sauran abubuwan da wutar ta lakume.
Mazauna sun shaida wa Zagazola, kwararre kan harkokin tsaro da yaki da ta’addanci a Yankin Tafkin Chadi cewa, ’yan gudun hijirar da ke sansanin sun yi kaura ne daga yankin Doron Baga da ke Karamar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno.
Ana zargin wutar girki ce ta yi sanadin tashin gobarar a safiyar Juma’a, lamarin da ya kara jefa ’yan Najeriyan cikin karin tashin hankali.