✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a ofishin INEC a Abuja

Gobara ta tashi a ofishin Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya da ke Abuja ranar Juma’a, gobarar ta kama ofishin Daraktan gudanar da zabe…

Gobara ta tashi a ofishin Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya da ke Abuja ranar Juma’a, gobarar ta kama ofishin Daraktan gudanar da zabe da kuma sashin harkokin jam’iyyu na hukumar.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar INEC Mista Oluwole Osaze-Uzzi, ya bayyana cewa kusa da inda gobarar ta tashi yana sashin cibiyar watsa labarai na hukumar ne kuma jami’an hukumar kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar.

Mista Oluwole, ya ce gobarar ba ta ci muhimman abubuwa ba sai dai kawai wasu kayan na’urorin ofis ne suka lalace sanadiyyar gobarar.

Majiyarmu ta samu rahoton cewa, gobarar ta fara ne da misalin karfe 11 na safe, inda aka samu nasarar kashe ta lokacin da jami’an hukumar kashe gobara suka halarci ofishin tare da jami’an bada agajin gaggawa (NEMA) reshen babban birnin tarayyya Abuja.

A jawabinsa Kwamishina kuma shugaban kwamitin ilmantar da masu zabe na Hukumar INEC Mista Festus Okoye, ya nuna rashin jin dadinsa game da tashin gobarar.

Sannan ya alakanta gobarar da tangardar wutar lantarki wanda ta haddasa sanadiyyar wasu kayan lantarkin suka kama da wuta.

“Wasu daga cikin ma’aikatan hukumar INEC suna ofishin lokacin da gobarar ta fara ci, sai wasu suka yi kokarin sanarwa da jami’an agajin kashe gobara na hukumar INEC kafin daga bisani su sanarwa ofishin hukumar kashe gobara ta  birnin tarayya, hakan ya sa aka samu nasarar kashe gobarar.” in ji Mista Festus.

Rahotan ya kara da cewa, duk wasu muhimman takardu ba su samu matsala ba.

 

Gobarar da ta ci ofis a hukumar INEC a Abuja