Wata gagarumar gobara ta tashi a masana’antar rigakafin cutar COVID-19 wato SII da ke birnin Pune na kasar Indiya.
SII daya ne da cikin manyan kamfanonin duniya masu yin magungunan rigakafi kuma Shugabansa, Adar Poonawalla, ya ce SII na shirin yin rigakafin COVID-19 guda biliyan daya a cikin shekara mai zuwa.
Babba Jami’in Hukumar Kashe gobara ta Pune, Prashant Ranpise, ya ce tabbbatar da tashin gobarar a ranar Alhamis kuma tuni aka tura ’yan kwana-kwana da suka ceto mutane daga ginin da aka samu gobarar.
“Jami’anmu na dubawa ko akwai wani wanda ya makale a wurin.
“Ba mu san abin da ya haddasa gobarar ba ko iya barnar da ta yi ba tukuna,’’ inji shi.
Sai dai wasu majiyoyi daga cibiyar hada rigakafi na SII sun ce gobarar ba ta shafi bangaren da ake kera allurar rigakafin COVID-19 mai suna wanda gwamnatin Indiya ta ba wa izinin gaggawa.