✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gobara ta tashi a kusa da Masallacin Annabi na Madina

Gobarar ta tashi a wani gine da ke kusa da Masallacin Harami na Madinah.

Gobara ta tashi a wani gini da ke kusa da Masallacin Harami na birnin Madina da ke Kasar Saudiyya.

Shafin Haramain Sharifain na Mahukunta Masu Kula da Masallatai biyu mafi alfarma a doron kasa na Makka da Madina, shi ne ya wallafa hakan a wani sako a dandalin sada zumunta na Facebook.

Sai da jami’an Hukumar Kashe Gobara sun ga bayan wutar yayin da tuni suka yi mata aiki da cikawa.

“Gobara ta tashi a kusa da Masjid Al Nabawi da ke Madinah, wacce jami’an tsaron cikin gida suka kashe cikin ’yan mintuna,” a cewar sanarwar.

Aminiya ta ruwaito cewa a makon jiya ne Mahukunta Masallatan Harami suka bayyana jerin Limamai shida da za su jagorancin sallolin Taraweeh da Tahajjud yayin Azumin bana a Makkah.